Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-01 21:37:59    
Yin barci ta hanyar kimiyya ya iya kiwon lafiya

cri

Kowa ya sani, tilas ne mutane su yi barci, amma awoyi nama ne da mutane suke bukata wajen yin barci a ko wace rana? Shugabar hadadiyyar kungiyar nazarin harkokin barci ta kasar Sin kuma shehun malama mai ilmin jikin dan Adam ta jami'ar ilmin likitanci ta Anhui madam Zhang Jingxing ta ce 'lokacin da mutane suke bukata wajen yin barci yana sha bamban da na ko wane mutum. Matsakaicin lokacin da wani baligi ya kan kashe wajen yin barci ya kai misalin awoyi 7 da rabi, amma awoyi 6 zuwa 9 ya yi. Kada wani ya mai da hankali kan awoyin da ya kashe wajen yin barci, idan ya ji dadi, ya ji karfi a jikinsa, to, lokacin da ya kashe wajen yin barci ya yi.'

A galibi dai, mutane sun iya kyautata lokacin yin barci bisa jikunansu. Amma binciken kimiyya ya shaida cewa, idan wani ya dade yana barci cikin dogon lokaci, za a kawo wa lafiyarsa illa, sa'an nan kuma, mai yiwuwa ne za a ba da tasiri kan ransa.

To, yaya za mu yi barci yadda ya kamata? Madam Zhang Jingxing ta nuna cewa, don yin barci yadda ya kamata, ana bukatar bin al'ada mai kyau a fannin yin barci. Ban da wannan kuma, madam Zhang ta yi nuni da cewa, yin barci a tsakiyar rana al'ada ce mai kyau ga mutane. Saboda tun daga wani mutum ya tashi da safe har zuwa ya yi barci da dare, ya yi ta bata karfi, idan ya huta kadan, za a sassauta gajiyar da yake fama da ita. Amma ta kuma shawarci cewa, kada a yi barci cikin dogon lokaci a tsakiyar rana.

Daga baya, za mu yi hira kan wasu matsalolin da muke fuskanta a fannin yin barci. Yin minshari da rashin barci su fi ta da hankulan mutane. An ce, mutanen kasar Sin da yawansu ya kai kashi 20 zuwa 30 cikin dari suna fama da yin minshari, wasu da yawansu ya kai misalin kashi 40 cikin dari suna fama da rashin barci. Wadannan cututtuka sun kawo wa lafiyar mutane barazana a duka jikuna da tunani, mutane da yawa sun san wannan sosai. 'na yi shekaru 5 zuwa 6 ina fama da yin minshari, a lokacin barci, na yi minshari da babbar murya, sa'an nan kuma, ban yi barci yadda ya kamata ba, na yi juwa a kwakwalwa, a karshe dai, ban iya tuna da abubuwa lami lafiya ba.'

'da ma na yi sufuri na dogon zango, na kan yi awoyi 24 ina aiki kullun, shi ya sa na fara fama da rashin barci. Ban lura da wannan ba, amma yanzu na kan yi barci har awoyi 3 zuwa 4 a ko wace rana kawai. Rashin barci ya tayar da hankalina sosai a lokacin da nake tuka mota.'

Yaya za mu warware wadannan matsaloli? Mataimakin darektan sashen ciwace-ciwacen numfashi na asibitin jama'a ta jami'ar Beijing Mr. Han Fang ya yi bayanin cewa, idan an yi minshari, wannan ya nuna cewa, an matsayiyyar hanyar numfashi; idan hanyar numfashi ta toshe, numfashi zai tsaya. 'saboda haka, yin minshari muhimmiyar alama ce ga mutanen da suke fama da ciwon tsayar da numfashi a lokacin barci, amma ba dukan mutanen da suka yi minshari su fama da yin minshari ba, bisa kididdigar da muka yi, mutanen da yawansu ya kai rubu'i su kan tsayar da numfashi a lokacin barci. Sa'an nan kuma, wadannan mutane da suka yi minshari ko da ba su tsayar da numshi a yanzu ba, amma mai yiwuwa ne za su fama da wannan matsala a nan gaba.'

Mr. Han ya kara da cewa, yanzu an yi amfani da injunan numfashi da kuma tiyata don shawo kan matsalar tsayar da numfashi a lokacin barci, an sami sakamako mai kyau.

A karshen bayaninmu, za mu tattauna kan rashin barci. Masu kamu da wannan ciwo ba su da isasshen lokacin barci, ko kuma ba su yi barci lami lafiya ba, ta haka, ba su yi aiki yadda ya kamata a rana ba.

Akwai dalilai da yawa da suka haddasa rashin barci, shi ya sa, muhimmin abu na shawo kan wannan ciwo shi ne gano dalilin rashin barci, daga baya, a shawo kansa. Sa'an nan kuma, ya fi kyau a shawo kan wannan ciwo tun da wuri. Kada wani ya sayi magani da kansa, a maimakon zuwa wurin likita, magungunan da suka sha su kan kawo musu illa.