Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-01 21:16:59    
Ana yin manyan nune-nune a Beijing don murnar ranar bikin 'yan kwadago na duniya

cri

Ran 1 ga watan Mayu ranar bikin 'yan kwadago na duniya ne. Yanzu ana gudanar da manyan nune-nune masu ban sha'awa na kasashe daban daban a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin don taya murnar ranar bikin nan.

Dakin nunin zane-zane na kasar Sin da ke a cibiyar birnin Beijing babban dakin nunin zane-zane ne daya tak bisa matsayin kasa a Sin. A lokacin da aka shirya shagalin shekarar al'adun kasar Faransa tun daga shekarar 2003 har zuwa ta 2004 a kasar Sin, an taba shafe kwanaki 38 ana yin babban nunin zane-zane masu daraja na kasar Faransa, yawan 'yan kallo da suka ziyarci wannan nuni ya wuce dubu 250. Yanzu kuma an sake fara yin nune-nune da ke karkashin lakabi haka "yanayin bazara a kasar Faransa" a dakin nunin zane-zane na kasar Sin. Malam Fan Di'an, shugaban dakin nunin zane-zanen nan ya bayyana cewa, "a hakika dai, kasashen Sin da Faransa aminai ne masu arziki a fannin fasaha. Ko da yake an kawo karshen shagalin shekarar al'adu da aka shafe shekaru uku ana yinsa a tsakanin Sin da Faransa, amma ana ganin cewa, Sin da Faransa dukansu kasashen fasaha ne masu dogon tarihi kuma masu arzikin kayayyakin fasaha. Sabo da haka shagalin shekarar al'adu da aka shirya a tsakanin kasashen biyu bai isa ba, ya kamata, a ci gaba da yin irinsa.

A gun wannan nuni mai suna yanayin bazara a Faransa, an nuna kayayyakin lu'ulu'u da yawansu ya wuce 300, daga cikinsu akwai kayayyakin lu'ulu'u da dawa wadanda ba a taba nuna su a sauran kasashe ba.

Ban da wannan dakin nunin zane-zane na kasar Sin, ana kuma yin "nunin kabilar Inca da kayayyakin masu daraja na kakanninsu" a dakin nunin tsoffin kayayyaki na kasar Sin da ke a wani gefen dandalin Tian'anmen da ke a cibiyar birnin Beijing. Al'adun kabilar Inca ta kasar Peru da ke a kudancin nahiyar Amurka sun shahara a duniya. Yau da shekaru 16,000 da suka wuce, dan adam sun riga sun fara zaman rayuwarsu a kasar Peru. A cikin wannan dogon lokaci, 'yan kabilar Inca sun sami al'adunsu masu haske. Malam Alvaro Roca-Rey Miro Quesada, shugaban dakin nunin tsoffafin kayayyaki na kasar Peru ya bayyana cewa, nunin nan da ake yi a birnin Beijing nunin al'adu ne mafi girma da kasar Peru ta shirya a nahiyar Asiya. Tsoffafin kayayyaki 248 da aka nuna a gun nunin nan dukansu masu aikin kula da tsoffin kayayyaki na kasar Peru suka zabe su daga wurare daban daban na kasar Peru a tsanake.

Bayan haka Malam Miro ya kara da cewa, mun shirya wannan nuni ne musamman domin bayyana tsohon tarihi na jama'ar kasar Peru. Bisa kokarin da muka yi, mun sami damar shirya wannan nuni a dakin nunin tsoffin kayayyaki na kasa ta Sin wanda shi ne dakin nuni mafi kyau. Mukasudin nuninmu shi ne domin jama'ar Sin za su fahimci tarihin ci gaba da jama'ar zamanin da ta kasar Peru suka samu har cikin sama da shekaru 5000 da suka wuce.

An ruwaito cewa, wata abar mafi daraja da aka nuna a gun wannan nuni ita ce wata tsohuwar wukar zinariya mai suna Tumi wadda a can can zamanin da aka taba amfani da ita wajen yin sadaukarwa ga Allah. A kan jikin wannan wuka mai siffar rabin wata da kotarta, an sassaka wani mutum-mutumin mala'ika mai fikafikai biyu wanda ya rungume hannaye biyu a gaban kirjinsa. Kuma yana saye da wata hula mai siffar rabin wata. Haka nan kuma an manna lu'ulu'u a kan kota da fikafikai da idanu da kunnuwan mutum-mutumin nan, kai wannan wuka tana da daraja kwarai.

Ban da wannan kuma, an gwada tangaran da kayayyakin zinariya da na saka masu yawa wadanda ke nuna yadda jama'ar zamanin da na kasar Peru suke yin aikin gona da na kiwon dabbobi da zaman yau da kullum.

Bayan da Madam Chen Hongdi wadda ta taba zamanta a kasar Peru a cikin shekaru da yawa da suka wuce ta ziyarci wannan nuni, ta bayyana cewa, "wannan nuni ya cancanci da a ziyarce ta. Ko da yake na yi shekaru da yawa ina aiki a kasar Peru, amma abin nadama shi ne, ban taba ganin irin wannan nuni ba. Yanzu, na ji matukar farin ciki da samun damar ziyarar nunin nan, na sake ganin kasar Peru. (Halilu)