Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-01 21:10:41    
An dauki matakai masu yakini domin ba da tabbaci ga jama'a dake yin hutu na dogon lokaci a bikin ma'aikata na ran daya ga Mayu a kasar Sin

cri

Sinawa sukan yi hutu na tsawon kwanaki 7 a kowace shekara a lokacin bikin ma'aikata na ran 1 ga watan Mayu na duniya. Sinawa masu yawan gaske sukan shirya bukukuwan aure da kuma harkokin haduwa na nishadi a duk tsawon wannan lokaci ; Ban da wannan kuma, mutane ba kadan ba sukan fita waje domin yin yawon shakatawa a wannan lokaci. Yanzu, wurare daban daban na kasar Sin sun riga sun dauki tsauraran matakai domin ba da tabbaci ga jama'a wajen yin hutu mai gamsarwa.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a 'yan shekarun baya, yawan mutanen da suka fita waje daga gidajensu domin yin yawon shakatawa a bikin ma'aikata na ran 1 ga Mayu ya zarce miliyan dari; An kuma kiyasta, cewa
Wadanda suke yin yawon shakatawa a wannan shekara sun fi na shekarun baya. Bisa wannan hali dai, hukumar kulawa da sa ido kan aikin kawo albarka ta kasar Sin da kuma ofishin kula da ayyukan hutu na duk kasa sun hada kansu da sassan da abun ya shafa na wurare daban daban na duk kasar domin kara karfin sa ido kan kwanciyar hankali na yawon shakatawa da kuma kawar da matsalolin hatsari.


Mr. Huang Yi, kakakin hukumar sa ido kan aikin kawo albarka ta kasar Sin ya bayyana cewa:'A duk tsawon lokacin hutu na ran 1 ga Mayu, wurare daban daban sun gudanar da harkokin duddubawa cikin tsanaki domin kawar da yiwuwar aukuwar hadari a wuraren yawon shakatawa ,da otel-otel kuma a fannin zirga-zirga. A duk tsawon lokacin nan, an tsara shirin riga-kafin matsalolin da kila za su auku ba zato ba tsammani'.


Alal misali: a shahararren wurin yawon shakatawa na ' Babbar Ganuwa' na Baijing, an kara bude hanyoyin mafita guda biyar domin samar da sauki ga masu yawon shakatawa, wadanda yawansu ya kai 60,000 a kowace rana. Jami'in wannan wurin shakatawa Mr. Wang Weidong ya fada wa manema labaru, cewa:'In an yi matsi a wuni wuri, to nan da nan za mu dauki matakin watsar da mutane domin tabbatar da kwanciyar hankali ga masu yawon shakatawa lokacin da suke morewa kan Babbar Ganuwa'.
A sannannen wurin yawon shakatawa na Tsaunin E Mei na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, da akwai mutane masu yawan gaske da suka je can domin morewa a bikin ma'aikatan ran 1 ga Mayu.
Wani jami'in hukumar tsaro ta lardin Sichuan mai suna Zhou Shaokun ya furta, cewa :'Mu kam mun rigaya mun fara aiki da tsarin ba da tabbaci ga samun kwanciyar hankali a lokacin da mutane masu yawon shakatawa suke yin hutu a wannan ni'imtaccen wuri, wato ke nan mun shirya ' yan sanda da yawa don su yi aikin tsaro ; Ban da wannan kuma, mun sanar da lambar tarho ta neman taimako cikin sa'o'i 24 daga ' yan sanda ga duk al'ummar kasar'.


Yanzu, ba a kawar da annobar cutar murar tsuntsaye ba kwata-kwata a kasar Sin. Saboda haka, hukumomin kasuwanci na kasar Sin sun riga sun nemi wurare daban daban na duk kasar da su kara kula da ayyukan musanye-musanyen abinci, da na hidima da kuma na sana'ar yanke dabbobi, ta yadda za a samu abinci mai tsabta. Lallai za a yanke hukunci mai tsanani ga kamfanoni da masana'anrtu, wadanda suka karya dokokin da abun ya shafa game da wannan.
A lokacin da ake gudanar da ayyukan tsaro da kyau a fannin yawon shakatawa da kuma abinci, sassan da abun ya shafa sun kuma nemi wurare daban daban na duk kasar da su tsara shirye-shiryen shagulgula da kuma shirye-shiryen gaggawa na ceto a duk tsawon lokacin da ake yin shagulgulan ranar bikin ma'aikata na ran 1 ga Mayu ko yin tarurukan haduwa na nishadi a wassu wurare, ta yadda wadannan wurare za su dace da sharadin kwanciyar hankali.( Sani Wang )