To, madalla jama'a masu karatu, yanzu za mu ci gaba da gabatar muku shirye shiryenmu, ga wannan shiri namu "Duniya ina labari", A ran 29 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao ya kammala ziyarar aikinsa a kasashe hudu wato kasar Saudi Arabiya da Moroco da Nigeria da Kenya.Kafin karshen ziyararsa, ministan harkokin waje na kasar Sin Mr.Li Zhaoxing ya gana da maneman labarun dake biye da ziyarar shugaban kasar Sin.inda ya karfafa cewa,wannan ziyarar da shugaban kasar Sin ya yi a kasashe hudu ta cika makasudin kara karfin zumuncin al'adar dake tsakanin sassa biyu da kara fahimtar juna da habaka yin aikatayya da kai wa juna moriya kuma da bude wani sabon halin ci gaban dangantakar aikatayya da kai wa juna moriya tsakanin kasar Sin da kasashe Larabawa da kasashen Afrika da na tsakanin kasashe masu tasowa, sabo da haka an iya cewa, wannan ziyarar aiki tana da muhimmanci sosai.
Bana shekarar cikon shekaru 50 da kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya tare da kasashe Larabawa da na Afrika. Daga ran 22 ga watan Afrilu, shugaban kasar Sin ya fara yin ziyarar aiki a kasashe hudu. A cikin ziyararsa, shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da yin musanye musanye tare da shugabanni na kasashe hudu kan dangantakar dake tsakanin kasa da kasa da matsalolin dake jawo hankulan sassa biyu. Kuma shugaba Hu Jintao ya yi muhimmin jawabi, ya kuma gana da shahararrun mutane na sassa daban daban. Bugu da kari kuma cikin ziyararsa, kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyi guda 28 na yin hadin guiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashe hudu kan sassan siyasa da na tattalin arziki da ciniki da na makamashi da na aikin ba da ilmi da kiwon lafiya da na al'adu da aikin shakatawa.
Wannan ministan harkokin waje ya bayyana cewa, wannan ziyarar da shugaban kasar Sin ya yi ta kara karfin fahimtar juna kan harkokin siyasa da kuma daga matsayin dangantakar dake tsakanin sassa biyu. A cikin manyan sauye sauyen da ake yi a kasashe su kansu da na duk duniya, a bayane ne shugaban kasar Sin ya gabatar da dangantakar abokantakar dabarun tsare tsare iri na sabon salo ta ingiza fahimtar juna kan siyasa da kai wa juna moriyar tattalin arziki da ba da gudumuwa kan harkokin duniya. Irin ra'ayin da ya gabatar ya sami yarda daga shugabanni na wadannan kasashe hudu.
Ya kuma ce, ziyarar da shugaban kasar Sin ya yi ta sa kasashe hudu su gabatar da shawarwari masu kyau wajen yin aikatayyar tsakaninsu da kasar Sin. Kuma yana fatan kamfanoni da yawa na kasar Sin za su zuba jari ga kasashe hudu don yin aikatayyar tattalin arziki, Kuma sassan masana'antu sun bayyana cewa, suna fatan kafa dangantakar abokantakar tattalin arziki na dabarun tsare tsare da na duk duniya. Bugu da kari kuma kasashe daban daban sun kuma nuna wa kasar Sin godiya saboda cikin dogon lokaci ne kasar Sin ta ba da musu gudumuwa cikin sahihanci. Kuma wadansu sassan watsa labaru sun bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin za ta kawo kyakkyawar damar neman bunkasuwar tattalin arziki ga Gabas ta tsakiya da babban yankin Afrika.
Ya kuma ce, cikin ziyararsa shugaban kasar Sin ya karfafa cewa,kasar Sin tana son tare da dimbin kasashe masu tasowa wajen kiyaye babban makasudi da ka'idoji na tsarin dokokin majalisar dinkin duniya, da kiyaye moriyar halal ta kasashe masu tasowa. A cikin ziyararsa, shugaban kasar Sin ya bayyana matsayin da kasar Sin ke rike da shi kan matsalar Gabas ta tsakiya, da matsalar karfin nukliya da ta kasar Iraq da ta kasar Iran da ta kasar Sudan.(Dije)
|