Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 20:02:02    
Halaye musamman 11 na shiri na 11 na shekaru 5 na raya kasar Sin

cri

Shiri na 11 na shekaru 5 wani kashi ne na shirin raya tattalin arzikin kasar Sin, muhamman abubuwan da aka tanada cikin shirin su ne an tsara tsarin manyan ayyukan gine-gine da barbazuwar 'yan kwadago da dangantakar da ke tsakanin sassan tattalin arzikin kasar, da tsai da makasudi da manufar dogon wa'adi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Ban da kasar Sin ta tsai da cewa, daga shekarar 1949 zuwa ta 1952 ya zama lokacin farfado da tattalin arzikin kasa, kuma daga shekarar 1963 zuwa ta 1965 ya zama lokacin daidaita tattalin arzikin kasar, daga shekarar 1953 zuwa yanzu ta riga ta tsara shirye- shirye guda 10 na shekaru 5 na raya kasar, a gun zama na 4 na babban taro na 10 na wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi kwanan baya, an zartas da tsarin ka'idoji na shiri na 11 na shekaru 5 na raya kasar. Jama'a masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu yi muku bayani kan muhimman halaye 11 na wannan shiri.

Halin musamman na farko shi ne, an tsara tsarin ka'idoji na wannan shiri bisa tunani na muhimman tsare-tsare a fannoni 2 wato ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya da samar da zaman al'umma mai jituwa.

Na 2, karo na farko ne tsarin ka'idojin ya raba takitocin raya kasa cikin jeri 2 wato na kimantawa da na kayyadewa, wannan ya bayyana cewa ba ma kawai ya kamata a mai da hankali kan takitocin tattalin arziki ba, kuma ya kamata a mai da hankali kan takitocin duk ayyukan al'adu tsakanin al'umma da na zaman al'umma da na muhalli.

Na 3, Tsarin ka'idojin ya sa aikin raya sabbin kauyukan zaman gurguzu a matsayi na farko na dukkan ayyukan muhimman tsare- tsare.

Na 4, An bayyana sosai cewa, muhimmin aikin da za a yi cikin shekaru 5 masu zuwa wajen bunkasa masana'antu ba kawai fadada sikelinsu ba ne, amma kyautata tsarinsu ne, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasa masana'antun kasar Sin daga masu girma zuwa masu karfi.

Na 5, A karo na farko ne tsarin ka'idojin ya mai da sana'ar yin hidima bisa muhimmin matsayi.

Na 6, Kan muhimman tsare-tsaren bunkasa yankunan kasa, an kara tabbatar da manufofi a fannoni 4 wato raya kasa a matsayi mai fifiko kuma mai muhimmanci da wadanda aka kayyade da kuma wadanda aka hana.

Na 7, Kan dangantakar da ke tsakanin mutun da halitta, an rubuta muhimman manufofi 2 na kasar wato yin tsimin albarkatun kasa da kiyaye muhalli cikin tsarin ka'idojin.

Na 8, Tsarin ka'idojin ya mai da aikin kirkire-kirkire cikin 'yanci da horar da mutane masu nagarta a kan muhimmin matsayi.

Na 9, Tsarin ka'idojin wani tsarin raya kasa ne, kuma wani tsarin yin gyare-gyare ne, ba ma kawai an kebe babi-babi guda 2 don yin bayani kan ayyukan kara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ba, a sauran babi-babi kuma da akwai abubuwan da suka shafi ayyukan gyare-gyare.

Na 10, Bisa tunanin raya kasa ta hanyar "hada fannoni 4 gu daya" wato tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman al'umma, tsarin ka'idojin ya kebe wani babi musamman domin bayyana ayyukan raya kasa wajen wayin kan siyasa da kyautata al'adu da raya zaman al'umma, kuma ya jaddada magana kan daukar mutun a gaban kome, da daidaita wasu manyan matsalolin da suka shafi moriyar jama'a sosai.

Na 11, Ban da wannan kuma an sabunta wasu abubuwa wajen siffar tsarin ka'idojin, ta yadda za a iya kara samun sauki wajen aiwatar da shi. (Umaru)