Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 20:02:02    
Kwararrun Sin da waje za su shugabanci aikin tsara shirin bikin budewar wasannin Olympics na Beijing da bikin rufewarsa

cri

An shirya wasannin Olympics cikin nasara ko a'a, bikin budewarsa ya kan taka wata muhimmiyar rawa. Yaya za a shirya bikin budewar wasannin Olympics na birnin Beijing a shekarar 2008? Domin tabbatar da cewa, za a shirya wani kyakkyawan bikin, a 'yan kwanakin baya, kwamitin wasannin Olympics na Beijing ya kafa wata babbar kungiyar tsara shirin bikin budewar wasannin Olympics da kuma bikin rufewarsa, wadda take kunshe da kwararru na kasar Sin da kasashen waje.

Kwamitin wasannin Olympics na duniya ya yi hasashen cewa, yawan mutanen da za su kalli wasannin Olympics da za a shirya a birnin Beijing a shekarar 2008 ta telibijin zai kai biliyan 3, idan ana son a sami yabo daga wajensu, to, wannan ya zama wani aiki mai wuya. A ran 16 ga wata, kwamitin wasannin Olympics na Beijing ya sanar da kungiyar tsara shirin bikin budewar wasannin Olympics na Beijing da kuma bikin rufewarsa.

A cikin wannan kungiya, mutumin da ya fi jawo hankulan jama'a shi ne babban jagora Zhang Yimou ya fi, wanda ya jagoranci manyan film da yawa. A hakika dai, shirin nishadi na mintoci 8 da aka nuna a bikin rufewar wasannin Olympics na Athens a shekarar 2004 shi ne Zhang Yimou ya jagora. Mr Zhang ya taba yin manyan film da yawa kamar 'Honggaoliang' da 'dahongdenglonggaogaogua' da dai sauransu, wadanda suka sami yabo sosai a duk duniya, sabo da haka ana ganin cewa, Zhang Yimou ya zama wani wakilin Sinawa a duk duniya a kan film. Wata bayananniyar alama ta film na Zhang Yimou ita ce Zhang ya kan nuna al'adun gargajiya na kasar Sin a cikin film dinsa, haka kuma Zhang Yimou ya iya sanya jama'ar kasa da kasa su fahimci wadannan al'adun Sin da kuma yabo a kan al'adun. Wannan kuma ya zama wani muhimmin dalilin da ya sa aka zabe shi da ya zama babban jagoran bikin budewar da rufewar wasannin Olympics na Beijing.

Ban da Zhang Yimou, shahararren jagoran film na Hollywood na kasar Amurka Steven Spielberg ya zama mai ba da shawara a cikin kungiyar tsara shirin bikin budewa da rufewar wasannin Olympics na Beijing. Idan ana son bayyana al'adun Sin, sai a zabi Zhang Yimou, to, idan ana son an hada al'adun Sin da duniya, to, za a iya  zaben Steven Spielberg. Bayan da ya karbi takardar aiki, Mr Spielberg ya yi farin ciki sosai, ya ce, yana son yin kokari tare da sauran mambobin kungiyar domin nunawa jama'a wani kyakkyawan bikin budewa da rufewar wasannin Olympics a Beijing a shekarar 2008.

Ban da Zhang Yimou da Steven Spielberg, kungiyar tana da sauran manyan kwararrun al'adu da yawa, kamar shugaban tawagar kide-kide da rawaye ta rundunar sojan suncin jama'ar Sin Zhang Jigang da kuma Chen Weiya da Ji Xianlin da Tang Yijie da Jin Shangyi da Xu Xiaozhong da kuma Chen Kaige da dai sauransu a kan al'adu daban daban.

Bisa burin kwamitin wasannin Olympics na Beijing, a gun bikin budewa da rufewar wasannin, za a bayyana ra'ayin 'duniya daya, mafarki daya' da 'samun jituwa', a sa'i daya kuma za a bayyana ruhun wasannin Olympics.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na Beijing Liu Qi ya ce, ingancin bikin budewar wasannin Olympics da za a shirya a birnin Beijing a shekara 2008 zai bayar da tasiri sosai ga ko kasar Sin za ta iya shirya kyakkyawan wasannin Olympics ko a'a. Ya ce, 'Jama'ar kasar Sin biliyan 1 da miliyan 300 suna sanya ran alheri ga wasannin Beijing, kuma suna mai da hankali sosai a kan ingancin bikin budewarsa. Jama'ar duniya da yawa su ma suna zura ido a kan bikin budewa. Muna fata ta bikin budewarsa, za a iya bayar da wata alama mai kyau ga 'yan wasanni da sauran baki da suka zo daga kasashe daban daban.'(Danladi)