Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 19:58:09    
Shugabannin kasashen Sin da Kenya dukansu sun yarda da ci gaba da zurfafa  hadin gwiwar sada zumunta tsakanin bangarorin biyu a fannoni daban daban

cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao, wanda yake yin ziyarar aiki a kasar Kenya ya yi shawarwari tare da takwaransa na Kenya Mwai Kibaki jiya a Nairobi, inda suka bayyna, cewa za su dukufa tare wajen yalwata kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa mai dorewa ta samun moriyar juna tsakanin kasashen Sin da Kenya da kuma ci gaba da zurfafa hadin gwiwar sada zumunta tsakanin bangarorin biyu a fannoni daban daban.
A gun shawarwarin, Hu Jintao ya furta, cewa kasar Sin tana mai da hankali sosai kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya ; Sa'annan ya gabatar da shawarwari guda hudu don kara karfafa dangantakar hadin kai dake tsakanin bangarorin biyu. Shawara ta farko, ita ce a nace ga yin musanye-musanye tsakanin manyan jami'ai da kuma ma'aikata domin yin musayar ra'ayoyi kan maganganun kasa da kasa da na shiyya-shiyya, wadanda suka jawo hankulansu duka, da kuma ci gaba da yin sulhuntawa tsakanin bangarorin biyu a M.D.D. da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa ; Shawara ta biyu ita ce, a nuna himma da kwazo wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai ; Shawara ta uku ita ce, a kara yin hadin gwiwa tsakaninsu a fannin al'adu da ilmantarwa, da kiwon lafiya da kuma na yawon shakatawa ; Shawara ta hudu wato ta karshe ita ce, a kara yin hadin kai bisa muhimman tsare-tsaren dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika,da kuma sanya kokari tare don tabbatar da samun nasara a gun taron koli na wannan dandalin tattaunawa da za a yi a watan Nuwamba na wannan shekara a nan Beijing.
Daga nasa bangaren, shugaba Kibaki ya nuna godiya ga bangaren kasar Sin bisa taimakon da ya bai wa kasar Kenya. ( Sani Wang )