Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 10:51:50    
Dangantakar da ke tsakanin Sin da Kenya tana samun bunkasuwa lami lafiya

cri

A 'yan shekarun baya, dangantakar da ke tsakanin Sin da Kenya tana samu bunkasuwa lami lafiya. Bangarorin biyu suna kara yin cudanya da hadin kai a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da ba da ilmi da yawon shakatawa da dai sauransu, haka kuma suna da kyakkyawar makoma a kan hadin kai a fannoni daban daban. Daga ran 27 ga ran 29 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao yana kai wa kasar Kenya ziyarar aiki, tabbas ne wannan ziyara za ta kara sa kaimi ga dangantakar moriyar juna da ke tsakaninsu, wannan ziyara kuma za ta zama wata muhimmiyar alama ce a tarihin dangantakar da ke tsakaninsu.

Daga shekarar 1963 da kasashen Sin da Kenya suka kulla dangantakar diplomasiyya zuwa yanzu, dangantakarsu tana kara samu bunkasuwa. Musamman bayan da kasar Sin yi gyare-gyare a gida da bude kofa ga duniya, shugabannin kasashen biyu suna kara ganawa juna. Tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin da firayin ministan Sin na wancan lokaci Li Peng da tsohon firayin ministan Sin Zhu Rongji da shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo da dai sauransu sun taba ziyarar kasar Kenya, tsohon shugaban kasar Kenya ya taba ziyarar kasar Sin har sau 3. to, wadannan ganawa da suka yi sun kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu.

A watan Agusta na shekarar da ta gabata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Kenya Mwai Kibaki, lokacin da ya kawo wa kasar Sin ziyarar aiki. A cikin shawarwarin da suka yi, bangarorin biyu sun nuna yabo a kan nasarorin da suka samu wajen raya dangantakarsu, haka kuma sun bayyana cewa, za su yi kokari tare domin kara sa kaimi ga dangantakar hadin kai da ke tsakaninsu. Ziyarar da shugaban Hu yake yi a kasar Kenya ta zama karo na farko da shugaban kasar Sin ya ziyarci kasar Kenya cikin shekaru 10 da suka gabata. Wannan ziyara yana da muhimmiyar ma'ana a tarihi, tabbas ne za ta mayar da dangantakarsu a cikin wani sabon matsayi.

Bisa kididdigar da aka yi, a cikin shekaru 2 da suka shige, kasashen biyu sun riga sun daddale yarjejeniyoyin da yawansu ya kai 12, wadanda suka shafi tattalin arziki da fasahohi da yawon shakatawa da kiwon lafiya da ba da ilmi da dai sauransu. A karshen shekarar 2005, an kafa cibiyar nazarin Confucious a jami'ar Nairobi. Wannan ya zama cibiyar Confucious ta faro da aka kafa a Afirka. A karshen watan Fabrairu na bana, gidan rediyon kasar Sin ya fara watsa shirye-shiryen FM ta R&M a birnin Nairobi, wannan kuma ya zama karo na farko da kasar Sin ta watsa shirye-shiryen FM a ketare. A 'yan shekarun baya, Sin da Kenya sun sami nasarori da yawa wajen gama kai a kan yawon shakatawa, yawan Sinawa da suke ziyarar Kenya yana kara karuwa.

Ban da wadannan abubuwa da muka ambata, cinikayyar da kasashen biyu suka yi tana samu bunkasuwa cikin sauri. Bisa kididdigar da hukumar kwastan ta kasar Sin ta yi, an ce, a shekarar 2005, yawan kudaden da suka samu wajen yin cinikayya ya kai dala miliyan 475, wanda ya karu da kashi 29.7 da ke cikin dari na makamancin lokaci. A cikin shirye-shiryenmu, mu riga mu bayar da irin wannan bayani da yawa.

Tare da kara bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Kenya, kasar Sin ta riga ta zama wata muhimmiyar kasa bisa manufar zura idonta ga kasashen gabas. A watan Agusta na bara, minstan harkokin waje na kasar Kenya Raphael Tuju ya raka shugaban kasar domin ziyarar kasar Sin. Bayan haka, ya bayyana wa kafofin watsa labaru na Kenya cewa, game da Kenya manufar 'zura ido ga kasashen gabas' ta zama wata shawara da tilas ne kasar Kenya ta yanke bisa halin gaskiya.(Danladi).