Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 10:51:01    
Koyon Sinanci a kusa da gida, bayani game da "Kolejin Confucius" na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya

cri

Daga ran 27 zuwa 29 ga wannan wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai ziyarar aiki a kasar Kenya. A lokacin ziyarar zai gana da daliban da ke koyon Sinanci cikin Kolejin Confucius na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya. Kwanan baya, wakilinmu da ke kasar Kenya ya samu labari daga wajen wasu malaman koyarwa da dalibai na wannan Koleji, to jama'a masu sauraro yanzu za mu karanta muku wani bayanin da ya ruwaito mana daga Kenya.

Aminai masu sauraro, in ba a gaya muku ba, ba za ku yi tsammani cewa wakar da kuke saurara ta fito ne daga bakunan wasu daliban Afirka wadanda suka shafe 'yan watanni kawai suna koyon Sinanci ba. Sun zo ne daga Kolejin Confucius na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya. Kolejin nan ita ce kolejin Confucius ta farko da kasar Sin ta kafa a Afirka, haka kuma kolejin Confucius daya ce tak yanzu a Afirka, wanda yake dauke da dalibai bakaken fata guda 25 na karo na farko tun bayan kafuwarsa a ran 19 ga watan Disamba na shekarar da ta wuce, wato wadannan dalibai sun riga sun shafe watanni 4 suna koyon Sinanci. Ko da yake lokaci ba yi tsawo ba, amma sun riga sun iya gaishe-gaishen juna ta hanyar yin amfani da Sinanci sosai, kuma sun iya bayyana wasu abubuwan dake cikin zukatansu da Sinanci.

Shariffa Begam Noordin, wata daliba ce ta Kolejin Confucius na jami'ar Nairobi. Yayin da take bayyana dalilin da ya sa ta zabi hanyan koyon Sinanci, ta ce, "Dalilin da ya sa na zabi darasin koyon Sinanci shi ne sabo da ina sha'awar wannan harshe sosai. Ina son al'adun kasar Sin, kuma ina son mutanen kasar, dukkansu masu sada zumunta ne sosai."

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa bunkasuwar da aka samu a kasar Sin a kowace rana wajen bude kofa ga kasashen waje, harshen Sinanci yana nan yana ta kara zama wani muhimmin harshe a duk duniya baki daya. Yawan baki da suke koyon Sinanci yanzu ya riga ya wuce miliyan 30 a duk duniya. Domin biyan bukatar da ake yi wajen koyon Sinanci, kasar Sin ta fara kakkafa "Kolejojin Confucius" a duk duniya baki daya musamman domin barbaza harshen Sinanci da al'adun kasar Sin. Bayan da kasar Sin ta kafa Kolejin Confucius na farko a shekarar 2004 a birnin Seoul, hedkwatar kasar Korea ta kudu, kuma ta kafa Kolejojin Confucius fiye da 10 a nahiyoyin Amurka da Turai da Afirka daya bayan daya. Don su daliban Afirka kuwa mafitarsu daya ta koyon Sinanci a da ita ce zuwa kasar Sin, amma yanzu an riga an sauya wannan hali.

Ko da yake daliban Afirka suna koyon Sinanci cikin himma da kwazo, amma nakaltar Sinanci da kyau ya zama wani babban kalubale gare su. Domin inganta sakamakon koyon Sinanci, malaman koyarwa Sinawa guda 2 na wannna koleji sun yi dabaru masu amfani da yawa. Madam Song Lixian, mataimakiyar shugabar kolejin Confucius ta ce, "Bayan darasin koyar da Sinanci, kuma mun bude darasin koyon al'adun kasar Sin. Dalilin da ya sa muka yi haka shi ne sabo da kowa ya sani cewa, harsuna ba su rabuwa da al'adu. Tun da muka fara bude wannan darasi, mun riga mun shirya aikace-aikace masu ma'ana da yawa don bayyana al'adun kasar Sin."

Malama Song ta kuma bayyana cewa, da yake mutanen kasar Kenya wadanda suke son koyon Sinanci sai kara yawa suke, shi ya sa sun tsara shirin kara yawan ajujuwa da suke da su wato daga daya kawai na yanzu na kolejin Confucius zuwa 2 ko 3, har ma a nan gaba kadan za mu dauki dalibai daga sauran kasashen Afirka.