Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-27 19:59:45    
Hu Jintao ya ba da jawabi a zauren majalisar dokoki ta kasar Nijeriya

cri

Yau, wato ran 27 ga wata, shugaba Hu-jintao na kasar Sin wanda ke ziyara a abuja, ya bayar da wani jawabi a zauren majalisar dokoki ta kasar Nijeriya. Sunan jawabin shi ne "yin kokari tare domin yalwata sabuwar dangantakar abokai mai muhimmanci a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin."Cikin jawabinsa, shugaba Hu ya yi bayani kan manufofin da gwamnatin kasar Sin take dauka domin neman yalwata dangantakar da ke tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin.

Shugaba Hu ya yi nuni da cewa, yanzu kasashen duniya na kara bai wa juna goyon baya, kuma suna kara samun haduwar moriyar juna. Domin neman bunkasa sabuwar dangantakar abokai a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, kamata ya yi, bangarorin 2 su nuna imani ga juna a wajen fanin siyasa, su yi kokari su kara amfanawa juna a wajen tattalin arziki, su yi koyi da juna a wajen al'adu, kuma su kara yin hadin gwiwa da juna a wajen aikin tsaro.

Shugaba Hu ya jadada cewa, abin da ya faru ya tabbatar da cewa, bunkasuwar da kasar Sin ta samu irin na lumana da hadin gwiwa ne. Bunkasuwar kasar Sin ba za ta kawo barazana ga sauran kasashe ba, abin da ta kai wa kasashen duniya kawai shi ne damar samun bunkasuwa.

Ban da wannan kuma, shugaba Hu ya ce, a watan Nuwamba na bana, za a kira taron dandalin hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda shugabannin kasashen Afirka da na kasar Sin za su bayar da hadaddiyar sanarwa, kuma za a shirya hadin gwiwar da kasashen Afirka da kasar Sin za su yi a shekaru 3 masu zuwa. A gun taron da za a yi, kasar Sin za ta yi bayani kan matakan da za ta dauka domin karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin.(Bello)