A ran 27 ga wata, bi da bi ne shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Najeriya ya gana da shugaba Menechukwu Nnamani na majalisar dattijai ta kasar Najeriya da shugaba Aminu Masari na majalisar wakilan dokokin kasar Najeriya, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a kara raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kara yin musanye-musanye a tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu.
Mr. Hu ya ce, bangaren kasar Sin yana mai da hankali sosai kan yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Najeriya. Yana fatan majalisun dokokin kasashen biyu za su ci gaba da yin hadin guiwa da kara yin mu'ammala a tsakanin ma'aikatansu.
Shugabannin majalisun dokokin kasar Najeriya sun bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu na ta samun karfafuwa a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yanzu irin wannan dangantaka tana cikin hali mai kyau a tarihi. Hadin guiwar tattalin arziki a tsakaninsu za ta kawo wa jama'ar kasashen biyu da jama'ar kasashen yammacin Afirka fatan alheri. (Sanusi Chen)
|