A yayin da shugaban kasar Sin Hu Jintao zai kai ziyarar aiki a kasar Nijeriya, wani wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya yi hira da mutane daga bangarori daban daban na kasar Nijeriya. Lokacin da suka tabo magana a kan muhimmiyar huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, gaba daya ne suke ganin cewa, huldar da ke tsakanin kasashen biyu tana kara kyautatuwa, kuma ya kasance da makoma mai kyau a wajen bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu.
Yayin da ake yin hira da shi, shugaban kungiyar sada zumunta tsakanin kasar Nijeriya da ta Sin wanda kuma tsohon jakadan Nijeriya ne a nan kasar Sin, wato Ambassado Chibendu. Ya bayyana cewa, muhimmiyar huldar da ke tsakanin Sin da Nijeriya tana bunkasa lami lafiya, kuma za ta kara kyautatuwa. Ya ce, a cikin shekaru 35 da suka wuce tun bayan da Nijeriya da Sin suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi ta bunkasa lami lafiya. Musamman ma a cikin 'yan shekarun nan, manyan kusoshin kasashen biyu sun yi ta kai wa juna ziyara, kuma bangarori daban daban na kasashen biyu sun yi ta cudanya da juna, huldar da ke tsakanin kasashen biyu tana bunkasa cikin sauri. Ya ce, 'amincewa da juna a fannin siyasa da moriyar juna a fuskar tattalin arziki da kuma taimakon juna a cikin harkokin duniya sun riga sun zama muhimman halaye na huldar da ke tsakanin Nijeriya da Sin.' Yana kuma cike da imanin cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin Hu Jintao zai kai a Nijeriya za ta ciyar da muhimmiyar huldar da ke tsakanin Nijeriya da Sin gaba zuwa wani sabon matsayi, ya kuma yi fatan kasashen biyu za su ci gaba da tallafa wa juna a cikin harkokin duniya, don neman tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa na duk duniya.
Bayan haka kuma, wani babban manazarci da ke aiki a hukumar nazarin al'amuran duniya ta Nijeriya, ya ce, Sin kasa ce da ta fi kowace kasa wajen yawan mutane a duniya, a sa'i daya kuma, Nijeriya kasa ce da ta fi yawan mutane a nahiyar Afirka. Har kullum dai, kasashen biyu suna goyon bayan juna a cikin harkokin siyasar duniya, ya kuma yi fatan za a kara bunkasa huldar da ke tsakaninsu. Ya ce, 'takardar manufofin kasar Sin a kan Afirka' da gwamnatin kasar Sin ta bayar a farkon wannan shekara, ta sake bayyana matsayin da kasar Sin ta dauka na sada zumunta da hadin gwiwa da kasashen Afirka cikin sahihanci, tabbas ne za ta zamo alamar da za ta nuna hanyar da za a bi ta bunkasa huldar zumunci tsakanin kasashen Afirka da Sin daga dukan fannoni. Ya kuma kara da cewa, yayin da yake nazari a kan al'amuran duniya, ya fi mai da hankali a kan wasu 'alamu na kasar Sin', kuma manyan nasarorin da aka samu a wajen aikin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekaru sama da 20 da suka wuce sun burge shi sosai. 'kasar Sin ta zamo misali ga Nijeriya da kuma kasashen Afirka masu yawa.'
Wani dan kasuwa mai suna Sulaiman wanda ya yi shekaru da dama yana yin ciniki da kasar Sin, ya ce, yayin da Sinawa suka zo nahiyar Afirka a karni na 15, sun kawo wa mutanen Afirka silki da ti da fadi-ka-mutu da dai sauransu. Yayin da yake cudanya da Sinawa, ya gane cewa, kasar Sin aminiya ce ta Afirka, wadda kuma ake iya amincewa da ita. Ya ce, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun ba da taimako ga sha'anin neman 'yancin kan Afirka ba, hatta ma sun ba da taimako sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka. Ya kuma yi imanin da cewa, ba ma kawai ziyarar Hu Jintao za ta kara sa kaimi ga bunkasa huldar da ke tsakanin Nijeriya da Sin da kuma cinikin da ke tsakaninsu ba, har ma za ta kara fadada hanyoyin Nijeriya da na kasashen Afirka baki daya wajen kau da talauci da kawo albarka.(Lubabatu Lei)
|