Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-27 09:55:51    
(Sabunta) Hu Jintao ya yi shawarwari da Olusegun Obasanjo

cri

A ran 26 ga wata da maraice, agogon Najeriya, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ya isa birnin Abuja a wannan rana da yamma domin fara yin ziyararsa ta aiki a kasar ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Najeriya Mr. Olusegun Obasanjo, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Najeriya bisa manyan tsare-tsare da maganganun kasashen duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu tare. Sun amince da cewa, za su tsara shirin bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare domin kara ciyar da dangantakar abokantaka da ke tsakanin Sin da Najeriya gaba bisa tushen ambata fasahohin da aka samu.

Hu Jintao ya jaddada cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Najeriya. Ta kan sa dangantakar da ke tsakanin Sin da Najeriya kan wani muhimmin matsayi lokacin da kasar Sin take raya huldar da ke tsakaninta da sauran kasashen duniya. Sabo da haka, Mr. Hu ya bayar da shawarce-shawarce guda 4. Da farko dai, kara amincewa da juna kan harkokin siyasa domin cimma burin kara yin hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare. Sannan kuma, kara bude fannonin yin hadin guiwa domin cimma burin neman moriya tare, musamman kara yin hadin guiwa a fannonin aikin gona da raya albarkatun halittu da samar da wutar lantarki da raya ayyukan yau da kullum da dai sauransu. Bugu da kari kuma, kara yin hadin guiwa da musanye-musanye a fannonin zaman al'umma domin cimma burin sada zumunta a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Daga karshe dai, Mr. Hu ya ce, ya kamata a kara yin hadin guiwa kan harkokin duniya domin cimma burin tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa a duk duniya.

Mr. Obasanjo ya bayyana cewa, yana maraba da zuwan Hu Jintao a kasar Najeriya. Ziyarar da Hu Jintao ke yi a kasar Najeriya ta bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu tana samun ci gaba yadda ya kamata. Ya kuma yarda da ra'ayoyin da Hu Jintao ya bayar.

Bayan da suka yi shawarwari, Hu Jintao da Olusegun Obasanjo sun halarci bikin rattaba hannu kan takardun hadin guiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da al'adu da kiwon lafiya a tsakanin kasashen biyu.

A wannan rana da dare kuma, Hu Jintao ya halarci liyafar da shugaba Obasanjo ya shirya masa musamman. (Sanusi Chen)