Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-26 22:46:09    
Hu Jintao ya isa Abuja domin fara yin ziyarar aiki a kasar Najeriya

cri

Bisa labarin da wakilanmu suka aiko mana, an ce, bisa gayyatar da shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Najeriya ya yi masa ne, a ran 26 ga wata da yamma, agogon Najeriya, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya isa birnin Abuja cikin jirgin sama na musamman domin fara yin ziyararsa ta aiki a kasar Najeriya. Shugaba Obasanjo ya je filin jirgin sama ya shirya gaggarumin bikin maraba da zuwan Hu Jintao da hannu biyu.

A cikin jawabin da ya yi a rubuce a filin jirgin sama na Abuja, shugaba Hu ya ce, bayan kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Najeriya har na tsawon shekaru 35, dangantakar da ke tsakaninsu ta samu ci gaba sosai. Bangaren kasar Sin yana darajanta dangantakar da ke tsakaninta da kasar Najeriya, kuma yana son hada kai da bangaren Najeriya kan yadda za su yi kokarin ci gaba da yunkurin da ake yi domin samu ingacciyar makoma da ciyar da hadin guiwa irin ta sada zumunta a tsakaninsu gaba.

Lokacin da yake yin ziyara a kasar Najeriya, Hu Jintao da Olusegun Obasanjo za su yi shawarwari, kuma zai gana da shugabannin majalisun dokokin kasar Najeriya da sauran abokan kasar.

Mr. Hu ya bayyana cewa, yana fatan wannan ziyara za ta kara sada zumunta da aminci a tsakanin bangarorin 2, kuma za ta karfafa abutar gargajiya da ke kasancewa a tsakaninsu. Sannan kuma, za a iya kara yin hadin guiwar moriyar juna a fannoni daban-dabam a tsakanin kasashen biyu. Sakamakon haka, za a iya ciyar da dangantakar abokantaka da ke kasancewa a tsakanin Sin da Najeriya gaba bisa manyan tsare-tsare. (Sanusi Chen)