Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-26 21:32:06    
Kasar Sin na shirin yin kwaskwarimar ' Doka kan masu laifuffuka ' domin kara karfin yanke hukunci ga masu laifin haddasa matsalar aikin kawo albarka

cri

Yanzu, hukumomin kafa dokoki na kasar Sin suna nan suna cikin shirin yin kwaskwarimar ' Doka kan masu laifuffuka' domin hana karuwar yawan matsalolin aikin kawo albarka da sukan auku a ' yan shekarun baya. Muhimmin batun da za a gyara, shi ne ta yaya za a kara karfin yanke hukunci ga masu barkata laifuffukan haddasa matsalolin aikin kawo albarka; Ban da wannan kuma, za a tanadi abubuwa a fili a game da yadda za a tabbatar da laifuffuka da kuma yanke hukunci ga mutane masu cin hanci da rashawa a fannin kasuwanci da kuma masu halalta kudaden haram. Wannan ne karo na shida da aka yi kwaskwarimar ' Doka kan masu laifuffuka' tun bayan da aka gyara ta a shekarar 1997 daga dukkan fannoni.
An gabatar da daftarin kwaskwarimar wannan doka ne a karshen shekarar bara ga taron kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar duk kasar domin dudduba shi. Abubuwan da suka fi jawo hankulan mutane a cikin daftarin, batutuwa ne da suka shafi aikin kawo albarka lami-lafiya.
Kwanakin baya ba da dadewa ba, babbar hukumar sa ido kan ayyukan kawo albarka ta kasar Sin ta fayyace, cewa kodayake yawan matsalolin ayyukan kawo albarka da kuma yawan mutanen da suka rasa rayukansu cikin matsalolin sun ragu a cikin watanni uku da suka shige, amma kuma manyan matsalolin ayyukan kawo albarka sukan auku. Wassu manazarta sun bayyana, cewa muhimmin dalilin da ya sa akan gamu da wadannan matsaloli shi ne domin wassu mutane sukan yi sakaci da aiki.
Daftarin kwaskwarimar wannan doka zai tanadi, cewa za a kara karfin yanke hukunci mai tsanani ga wadanda sukan yi amfani da gine-gine da injuma marasa kyau, da tilasta wa sauran mutane don yin aiki cikin yanayi mai hatsari da kuma boye takamammen magana kan matsalolin ayyukan kawo albarka. Wa'adin hukuncin shekaru goma ne.
Mr. Zhou Kunlen, mataimakin daraktan kwamitin shari'a na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana, cewa:' Tabbas ne za a yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka haddasa manyan matsalolin ayyukan kawo albarka ; Ban da wannan kuma, za a gurfanar da mutane wadanda suka saba wa dokokin kula da ayyukan kawo albarka lami-lafiya, da haddasa matsalolin ayyukan kawo albarka da kuma jinkirtar da lokacin ceton ma'aikatan da suka jikata cikin matsalolin a gaban shari'a'.
Za a yi kwaskwarimar batutuwa guda ashirin dake cikin wannan ' Doka kan masu laifuffuka'. Gwamnatin kasar Sin za ta sanya matukar kokari wajen yaki da almubazzaranci a wannan shekara a fannin kasuwanci da na kudi.
Mr. An Jian, mataimakin daraktan kwamitin ayyukan shari'a na kwamitin din-din-din na Majalisar wakilan jama'ar duk kasar ya furta ,cewa: ' Ya kamata a yanke hukuncin shari'a ga ma'aikatan da ba na gwamnati ba daga kamfanoni da kuma masana'antu, wadanda suka yi amfani da mukamansu wajen yin musanye-musanye da iko da na kudi da kuma mutane wadanda suka lahanta moriyar al'ummar kasa'.
Ban da wadannan kuma, daftarin kwaskwarimar dokar ya fito da dabarun yanke hukunci ga danyen aikin yin zamba a fannin ba da rance, da sarrafe-sarrafen kasuwannin hada-hadar kudi da na sayar da kayayyakin da aka yi odarsu da kuma tauye moriyar masu zuba jari har da na halalta kudaden haram. ( Sani Wang )