Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-26 20:38:39    
Nightingale, jakadiyar da aka aiko daga sama zuwa duniyar bil Adama

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Suwaiba Tanimu daga birnin Yamai na kasar Nijer, wato mene ne asalin lambar yabo ta Nightingale.

Masu sauraro, malama Florence Nightingale ta kasance mutumiyar da ta shimfida harsashi a fannonin sana'ar nas ta mata da kuma ilmin jiyya na zamani. A ran 12 ga watan Mayu na shekara ta 1820, an haifi Florence Nightingale a wani gida mai arziki da ke birnin Florence na Italiya, kuma an ilmantar da ita kamar yadda ya kamata, har ma ta taba yin karatu a jami'ar Paris. A shekara ta 1850, duk da rashin amincewar iyalanta, Madam Nightingale ta je kasar Jamus don karanta ilmin jiyya, kuma ta fara yin nazari a kan ayyukan jiyya na kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da dai sauransu, har ma ta yi rubuce-rubuce da dama da suke shafar ilmin jiyya. Daga shekara ta 1854 har zuwa ta 1856, sojojin taron dangi na kasashen Birtaniya da Faransa da Turkiya sun yi fada da Rasha a yankin Crimea. Sabo da rashin nas nas da kuma ayyukan jiyya marasa inganci, shi ya sa yawan mutuwar sojojin Birtaniya da suka ji rauni ko ciwo ya kai har rabi. A cikin irin wannan hali ne, sai Madam Nightingale ta shugabanci nas nas zuwa asibitin da aka kafa a fagen yaki. Ta hanyar kyautata tsarin kula da asibiti da kuma inganta ayyukan jiyya, a cikin 'yan watanni kadan, sai yawan mutuwar masu jin rauni ya ragu har zuwa kashi 2.2%.

A cikin yakin Crimea, sabo da halinta na kirki da nuna jin kai da ta yi, Madam Nightingale ta yi wa sojoji na duk bangarorin biyu da ke fada da juna jiyya, shi ya sa sojojin na fagen yaki suna kiranta 'sarauniyar da ke rike da fitila'. Bayan da yakin ya kammala, an dauke ta a matsayin jarumar al'umma. A shekara ta 1860, Madam Nightingale ta yi amfani da asusun Nightingale da jama'a suka bayar, ta kafa makarantar koyon aikin nas ta Nightingale, wadda ta kasance makaranta ta farko a wajen horar da nas nas, wadda kuma ta sa kaimi ga bunkasuwar ayyukan jiyya da ayyukan horar da nas a kasashe daban daban na yammacin Turai, har ma a duk duniya baki daya. Rubuce-rubucenta dangane da asibiti da kuma aikin jiyya da dai sauransu kuma sun zama muhimman littattafan koyarwa a wajen ba da ilmin gudanar da asibiti da kuma horar da nas. Sabo da kokarinta, ilmin jiyya ya zama wani ilmi na musamman. Ra'ayinta dangane da ba da ilmin jiyya ma ya barbazu daga Birtaniya har zuwa kasashe daban daban na Turai da Amurka da kuma Asiya. Amma abin bakin ciki shi ne, a shekara ta 1901, sabo da tsananin gajiya, Madam Nightingale ta makance. Daga baya, a shekara ta 1907, don nuna yabo a kan babban taimakon da ta bayar a wajen aikin jiyya, sarkin kasar Birtaniya ya ba ta lambar yabo, sabo da haka kuma, ta zama mace ta farko da ta sami wannan girmamawa a Birtaniya. A shekara ta 1910, Madam Nightingale ta riga mu gidan gaskiya.

A shekara ta 1912, kungiyar nas ta duniya, wato ICN, ta tsai da ranar 12 ga watan Mayu, wato ranar haihuwar Nightingale, a matsayin ranar nas ta duniya, don sa kaimi ga nas nas da su bunkasa aikin nas, kuma su nuna kauna da hakuri da kulawa ga ko wane majiyyaci, su yi musu jiyya kamar yadda ya kamata.

Har wa yau dai, a wannan shekara, wato 1912, kungiyar Red Cross ta duniya ta tsai da kudurin cewa, za a fara ba da lambar yabo ta Nightingale a shekaru biyu biyu, a matsayin lambar yabo ta koli a duk duniya ga nas nas na kasashe daban daban. A gun taron wakilan kungiyar red cross ta duniya wanda aka yi a shekara ta 1991, an zartas da ka'idojin lambar yabo ta Nightingale, inda aka tanadi cewa, za a iya ba da wannan lambar yabo ga nas nas maza da mata da masu aikin sa kai da suka yi aikin jiyya, wadanda a lokacin yaki ko na lumana suka ba da babban taimako, kamar nuna bajinta da ra'ayin sadaukar da kansa, da kuma dukufa a kan ceton nakasassu da wadanda suka ji rauni da kuma wadanda yaki ya kawo musu barna.

Wang Xiuying mace ce ta farko da ta sami lambar nan ta Nightingale a nan kasar Sin. Ya zuwan yanzu dai, a nan kasar Sin, akwai nas nas 48 da suka sami wannan lambar yabo. (Lubabatu Lei)