
A ran 25 ga wata a birnin Rabat, bi da bi ne shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da firayin minista Driss Jettou da shugaban majalisar dattawa ta kasar Morocco Moustapha Okacha da shugaban majalisar wakilai ta kasar Morocco Abdelouahed Radi.
A yayin da shugaba Hu ya gana da Driss Jettou, ya bayar da shawarwari guda hudu domin kara sa kaimi ga hadin kansu a kan tattalin arziki da cinikayya, daya bayan daya: don kara yin cinikayya tsakanin bangarorin biyu da samun daidaiton ciniki, kasar Sin za ta kara shigar da kayayyaki daga kasar Morocco, kuma tabbatar da fannoni da suke gama kai a mataki na farko kamar a aikin gona da man fetur da gas da dai sauransu, kuma za su kara sa kaimi ga hadi kai a kan kwangila da kara habaka fannonin da suke gama kai, guda hudu da kara gama kai a kan yawon shakatawa da kara yin cudanyar jama'a.

Driss Jettou ya yarda da wadannan shawarwari hudu da shugaba Hu ya gabatar da su.
A yayin da shugaba Hu ya gana da shugabannin majalisu biyu, shugaba Hu yana fata bangarorin biyu za su kara yin cundanyar majalisunsu domin kara bayar da gudumowwa ga dangantakarsu da hadin kansu.(Danladi)
|