A ran 25 ga wata a birnin Rabat, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da firayin ministan kasar Morocco Driss Jettou, inda shugaba Hu ya bayyana cewa, yana fata za a kara gama kai irin na moriyar juna a kan tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasashen biyu, haka kuma za a kara nazari a kan sababbin hanyoyi da bangarorin biyu suka gama kansu.
Don kara sa kaimi ga hadin kansu a kan tattalin arziki da cinikayya, shugaban Hu ya bayar da shawarwari guda hudu, daya bayan daya: don kara yin cinikayya tsakanin bangarorin biyu da samun daidaiton ciniki, kasar Sin za ta kara shigar da kayayyaki daga kasar Morocco, kuma tabbatar da fannoni da suke gama kai a mataki na farko kamar a aikin gona da man fetur da gas da dai sauransu, kuma za su kara sa kaimi ga hadi kai a kan kwangila da kara habaka fannonin da suke gama kai, guda hudu da kara gama kai a kan yawon shakatawa da kara yin cudanyar jama'a.
Driss Jettou ya yarda da wadannan shawarwari hudu da shugaba Hu ya gabatar da su.(Danladi)
|