Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-25 19:17:52    
An sami ci gaba wajen share fage domin taron baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai na kasar Sin

cri

A gun taron manema labarun da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 24 ga wata a nan birnin Beijing, an yi bayani kan nasarar da aka samu wajen ayyukan share fage domin taron baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai na kasar Sin. Hukumar ci gaban cinikin kasashen duniya ta kasar Sin da jami'an gwamnatin birnin Shanghai sun yi bayani a gun taron cewa, yanzu ana nan ana samun ci gaba wajen ayyukan share- fage domin taron baje-koli na Shanghai, da akwai kasashe da kungiyoyin duniya 14 wadanda suka tabbatar da cewar za su halarci taron. An ce, za a yi kokarin samun balas tsakanin kudin shiga da na kashewa wajen yin taron baje-koli ta hanyar bude tasuwanni. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.

Za a yi taron baje-koli na duniya a shekarar 2010 a birnin Shanghai, birnin masana'antu da kasuwanci mafi girma na kasar Sin, wannan ne karo na farko da aka shirya wannan babban taron baje-koli a kasashe masu tasowa. Babban take na wannan taro shi ne, "A kara jin dadin zaman birane", wato za a tattauna maganar yadda za a kyautata taimakon da biranen ke bayarwa, da kafa dangantaka mai jituwa a tsakanin birane da kauyuka da kuma muhallin halittu.

A gun taron manema labarun da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 24 ga wata, madam Gao Yan, mataimakiyar hukumar ci gaban cinikin kasashen duniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da muhimmanci sosai kan ayyukan share fage domin wannan taron baje-koli, kuma ta riga ta gayyaci kasashe daban-daban na duniya don su shiga taron. Ta ce, "Kwanan baya gwamnatin kasar Sin ta riga ta aike da sakonni wadanda firayim minista Wen Jiabao na majalisar gudanarwa da ministan harkokin waje Mr. Li Zhaoxing suka sa hannu bi da bi zuwa kasashe 166 da kungiyoyin kasashen duniya da yawansu ya kai kusan 50 don gayyatar kasashe daban-daban na duniya da kungiyoyin kasashen duniya da abin ya shafa da su zo nan kasar sin don halartar wannan taron baje-koli."

An ce, zuwa yanzu, da akwai kasashe 13 ciki har da Faransa da Ukraine da Bahren da kuma sakatariyar yarjejeniyar ire-iren tsire-tsire wadanda suka tabbatar da cewa za su halarci taron. Ban da wannan kuma da akwai gwamnatocin kasashe da kungiyoyin kasashen duniya da yawa wadanda suka bayyana burinsu na yin kokarin halartar taron, wasu daga cikinsu kuma sun riga sun tabbata cewa za su halarci taronn.

Yanzu, birnin Shanghai ya riga ya tsai da shirin bude kasuwanni a gun taron baje-koli, ciki har da ayyukan ba da taimako ga tamburan kayayyaki da yin hidima wajen kasuwanci. Bisa shirin da aka tsayar an ce, taron baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai zai dauki abokan hadin gwiwa da yawansu ya kai 10 zuwa 15, da manyan 'yan kasuwa masu ba da taimako guda 12 zuwa 20. Mr. Yang Xiong, mataimakin shugaban birnin Shanghai ya bayyana cewa, "Jimlar kasafin kudin kashewa da aka yi a gun wannan taron baje-koli na duniya ta kai kudin kasar Sin wato Yuan biliyan 10.6. Yawancin kudin shiga da za mu samu za su zo ne daga tikitocin da za a sayar, an kimanta cewa wannan adadi zai kai wajen Yuan biliyan 6. Kuma muna fatan za mu samu taimako domin rage yawan kudin da za a yi hasararsu ta hanyar aiwatar da shirin yin hada-hadar kudi."