Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-25 18:53:02    
Dandana abincin gargajiya irin na kasar Rasha a birnin Harbin na kasar Sin

cri

Yau da shekaru sama da 100 da suka wuce, Rashawa dubbai sun yi doguwar tafiya daga gabar Kogin Volga a nahiyar Turai zuwa birnin Harbin da ke gabar Kogin Songhuajing a arewacin kasar Sin, sun fara zamansu a birnin Harbin. Yanzu, ban da gine-gine irin na gargajiyar Rasha da yawa da aka gina a cikin wannan birni da ya shahara wajen sanyi, kuma akwai dakunan cin abinci irin na gargajiyar Rasha da yawa.

Daga cikin wadannan dakunan cin abinci, akwai biyu da ke cibiyar birnin wadanda suka fi shahara. Rashawa ne suka kafa su a farkon karni na 20. Daya daga cikin shahararrun dakunan cin abincin nan biyu, sunansa Huamei. Wani tsoho mai suna Wang Wenli wanda shekarunsa ya kai 75 da haihuwa a bana, ya shafe shekaru 40 ko fiye yana aiki a cikin wannan dakin cin abinci irin na gargajiyar Rasha. Ya kan bayyana wa masu cin abinci wani labari mai ban sha'awa cewa, "kamata ya yi, a ce, dakin cin abincinmu mai suna Huamei dakin cin abincin gargajiya irin na Rasha ne na farko da aka kafa a duk kasar Sin baki daya. Amma wani Bayahude na kasar Rasha ne ya kafa wannan dakin cin abincin tun shekarar 1925."

Yanzu, kayayyakin abinci da ake sayarwa a dakin cin abinci na Huamei ba su tashi daidai da na gargajiyar Rasha sosai ba. An riga an canja dadinsu don dacewa da Sinawa. Idan wani ya sami damar cin abinci a wannan daki, to, ya kamata, ya dandana shahararrun kayayyakin abinci da ake dafawa a wannan daki kamar miya da ake kira Borsch a Turance da jatan lande da sauransu. Bayan da wani Bajapane dan yawon shakatawa ya ci abinci a dakin nan a karo na farko, sai ya bayyana cewa,

"abinci irin na Rasha da na ci a dakin nan yana da dadi kwarai. Ina sha'awar shan miyar da ake yi a nan. Ban da wannan kuma, salati da jatan lande su ma suna da dacin ci. Haka zalika muhallin dakin nan ma yana da kyau, ya tashi daidai da na farkon karni na 20. A ganina, sigar dakin nan ita ce ta kasar Rasha sosai."

Idan wani ya bi ta babban titi na tsakiya zuwa arewa, to, zai ga wani karamin rawayen gini mai hawa biyu a gabashin mararrabar titin nan. Da ma gidan nan ya taba zama wani kantin sayar da kayayyakin zaman yau da kullum mai kayatarwa a birnin Harbin. Amma yanzu ba haka ba ne. An riga an mayar da hawa ta biyu don ta zama dakin karatu, amma a hawa ta daya, akwai wani dakin cin abinci irin na gargajiyar Rasaha wadda ake kira "Russia ta 1914.

Da aka shiga cikin wannan dakin cin abinci, za a ga wani zanen fanti na wata mace ta kasar Rasha da aka manna a kan bango da ke fuskantar kofar dakin nan. Mai dakin cin abincin nan Hu Hong barbarar yanyawa ne na Sin da Rasha. Hu Hong ya bayyana cewa, wannan mace ta kasar Rasha kakar mahaifiyarsa ce. Ya ce, ya fi so ya mayar da dakin cin abincinsa da ya zama wani dakin tunawa da iyalai don tunawa da Rashawa sama da dubu 200 wadanda suka taba zamansu a birnin Harbin. Ya ce, "ina sha'awar tsoffin gine-gine irin na gargajiyar kasar Rasha, da na sami wannan daki, sai na yi masa kwaskwarima, na mayar da shi don ya zama dakin cin abinci. A ganina, duk wanda ya shiga cikin dakin nan, zai fahimci yadda wadannan Rashawa suka yi zamansu a kasar Sin a zamanin da."

Idan an kwatanta abinci da ake sayarwa a dakin cin abinci mai suna Russia da na Huamei, to, za a fahimci cewa, dadin abinci na dakin Russia ya fi na dakin Huamei zama na gargajiyar Rasha. An ce, tun can da akwai wata 'yar aikin gida na Hu ta kware wajen dafa abinci irin na gargajiyar kasar Rasha. Yanzu irin abinci da ake sayarwa a dakinsa ya tashi daidai da irin abinci da wannan 'yar aikin gida ta dafa. (Halilu)