A ran 24 da ran 25 ga wata a birnin Shanghai na kasar Sin, an yi taron fadin albarkacin bakinka kan maganar yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci na kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen Asiya da yankunan da ke bakin tekun Pacific. Gwamnatocin kasar Sin da Amurka ne suka shirya wannan taro tare. Mutane fiye da 110 ciki har da jami'ai da kwararru da suka zo daga rukunonin tattalin arziki 18 da wasu kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa wadanda suke kula da aikin yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci da wakilan hukumomin gwamnatin kasar Sin sun halarci taron. A gun taron, wakilai sun tattauna tare da yin musayar ra'ayoyi kan yadda za a yi hadin guiwa kan yunkurin yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci da kin shigowar da masu cin hanci da rashawa da maganar komar da dukiyoyin da aka handame da masu cin hanci da rashawa a kasarsu. Bangaren kasar Sin ya bayar da matsayi da matakai da take dauka domin hada kansa da kasashen waje kan yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci. Yanzu ga wani bayanin musamman da wakilinmu ya aiko mana daga birnin Shanghai.
Lokacin da ake bunkasa tattalin arziki bai daya a duniya ko a shiyya-shiyya, ana tafka laifin cin hanci da rashawa da al'amubazzaranci a tsakanin kasa da kasa kamar yadda ake yin cinikin waje ko zuba jari a tsakanin kasa da kasa. Yanzu maganar yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci da ke kasancewa a gaban dukkan kasashen duniya ta kasance mai sarkakiya. Mr. Li Yubing, mataimakin ministan sa ido kan ayyukan gwamnatin kasar Sin ya bayyana matsayin da kasar Sin take bi kan yadda za a yi hadin guiwa wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci. Mr. Li ya ce, "Gwamnatin kasar Sin na mai da hankali sosai kan yadda za a yi hadin guiwa a tsakaninta da kasashen waje wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci. Muna fatan za a kara yin hadin guiwa da kasashe da yankuna ciki har da hukumomin yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci na kungiyar hadin guiwar tattalin arziki ta Asiya da yankunan da ke bakin tekun Pacific bisa ka'idojin zaman daidai wa daida da moriyar juna da girmama bambancin da ke kasancewa a tsakanin kasashe da yankuna daban daban. Kasar Sin za ta yi kokari ba tare da kasala ba kan yadda za a ciyar da yunkurin yaki da rashawa da al'amubazzaranci gaba a yankunan Asiya da yankunan da ke bakin tekun Pacific."
A gun taron kuma, jakada Wang Xuexian wanda ke yin aiki a hukumar kula da harkokin yin hadin guiwa da kasashen waje a ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayar da matakan da kasar Sin ta dauka wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci. Mr. Wang ya ce, "Gwamantin kasar Sin ta yi kokari ta yi hadin guiwa da kasashen waje wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci bisa ka'idojin M.D.D. Kasar Sin ta riga ta sa hannu a kan 'Yarjejeniyar yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci ta M.D.D.' da 'Yarjejeniyar M.D.D. ta yin yaki da kungiyoyi masu laifuffuka a ketare'. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Sin tana hadin guiwa da kasashen waje a kai a kai, kuma ta riga ta daddale yarjejeniyoyin shari'a na samar wa juna taimako da kasashe 39 yayin da ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin komar da masu laifuffuka da kasashe 26."
Kasar Sin ta kara yin hadin guiwa da kasashen waje wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci, wannan ba ma kawai ta yi yaki da jami'ai wadanda suka yi laifin rashawa da al'amubazzaranci kuma suka gudu zuwa kasashen waje ba, har ma ta bayar da gudummawarta sosai ga sauran kasashen duniya wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci. Wannan taro kuma wani muhimmin mataki ne da aka dauka domin tabbatar da ra'ayin yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci da shugaba Hu Jintao na kasar Sin da shugaba George W. Bush na kasar Amurka suka samu lokacin da suka halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin guiwar tattalin arziki ta Asiya da yankunan da ke bakin tekun Pacific da aka yi a Santiago na kasar Chile a watan Nuwamba na shekara ta 2004. Madam Debra W. Yang, wakilin bangaren kasar Amurka kuma mai gabatar da kara na kasar Amurka ta yaba wa hadin guiwar da kasar Sin ta yi da kasar Amurka. Madam Yang ta ce, "Wannan taro wata muhimmiyar alama ce ga yunkurin cika alkawarin yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci tare ne da kasar Amurka da kasar Sin suka dauka. Ina fatan kasashen biyu za su ci gaba da yin musayar ra'ayoyinsu wajen yin yaki da rashawa da al'amubazzaranci." (Sanusi Chen)
|