Ran 19 ga watan Afril, majalisar dokokin kasar Korea ta Kudu ta kada kuri'a kan shirin nada sabon firaministan kasar, 'yar jam'iyyar Uri ta kasar madam Han Myung-sook ta sami yawancin kuri'u, don haka ta zama sabuwar firaministar kasar, ta haka, ta zama mace ce ta farko da ta zama firaministar kasar bayan da aka kafa kasar Korea ta Kudu a shekarar 1948 har zuwa yanzu.
Bisa labarin da ka bayar, an ce, 'yan majalisar dokokin kasar 264 sun jefa kuri'a ba tare da yin rajista ba a ran nan, inda wasu 182 suka amince da madam Han, yayin da wasu 77 ba su amince da ita ba. Madma Han Myung-sook firaminista ta uku ce ta gwamnatin kasar da ke karkashin shugabancin Mr. Roh Moo-hyun, ta fara aikinta a ran 20 ga wata a hukunce.
Kafin kada kuri'a, majalisar dokokin kasar ta yi kwanaki 2 tana shirya wani taron sauraron shaidu na musamman don nazarin mutanen da aka gabatar da su daga fannonin karfin tafiyar da ayyuka da ra'ayin siyasa da na diplomasiyya da kuma da'a. Madam Han ta sami yawancin kuri'u a ran 19 ga wata, wannan ya shaida cewa, yawancin 'yan majalisar sun gaskata da wannan firaminista ta farko bayan kafuwar kasar Korea ta Kudu.
An haifi Han Myung-sook a birnin Pyongyang na kasar Korea ta Arewa a shekarar 1944, ta kammala karatu a shahararriyar jami'ar mata ta Ewha. Tun daga shekaru 1970, madam Han ta himmantu ga ayyukan dimokuradiyya da mata, ta taba zama jami'ar kungiyoyin mata da ba na gwamnatin ba daya bayan daya. Ita wata mace ce mai afuwa, amma ta tsaya tsayin daka kan muhimman batutuwa, shi ya sa ta sami martaba daga al'ummar kasar sosai.
A shekarar 2000 da ta gabata, madam Han ta zama 'yar majalisar dokokin kasar ta zagaye na 16, ta fara ranta na siyasa a hukunce. Daga baya kuma, ta shiga majalisar ministocin kasar da ke karkashin shugabancin Mr. Kim Dae-jung, ta zama minista ta farko da ke kula da daidaita tsakanin maza da mata. A cikin wa'adin aikinta, ta ba da gudummowa wajen daga matsayi da rawar mata na kasar, ta hanyar tsara 'kundin catar daidaita tsakanin maza da mata na karni a 21' da gyara 'manyan dokoki na bunkasuwar mata' da kuma kara karfin 'dokar taimakon gwamnatin kan kiwon jarirai'. Bayan da Mr. Roh Moo-hyun ya kama karagar mulkin kasar, ya nada madam Han da ta zama ministar harkokin muhalli, sa'an nan kuma, kafofin yada labaru sun zabe ta da ta zama 'minista mafi nagarta a fannin shugabanci'.
Madam ta sake cin nasara a cikin zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka yi a shekarar 2004, ta fara gwada gwanintarta a cikin majalisar dokokin kasar da kuma jam'iyyar Uri, ta taba kama muhimman mukami.
A cikin rukunin siyasa na kasar Korea ta Kudu, madam Han Myung-sook ta nuna halin musamman na mata da karfin sa ido da yanke shawara. A lokacin da take kan mukamin ministar kula da daidaituwa tsakanin maza da mata da kuma ministar harkokin muhalli, madam Han ta ji dadin saurarar shawarce-shawarce na sauran mutane. Akasarin ra'ayoyin jama'a na ganin cewa, wadannan fifikon da take da su da kuma karfin daidaita dukansu sun zama dalilan da suka sa madam Han ta ci nasara a cikin kada kuri'ar da majalisar dokokin kasar ta yi.
Madam Han Myung-sook ta zama sabuwar firaministar kasar a cikin mawuyacin hali, kuma an danka mata babban nauyi bisa wuyanta. Za a yi zaben kananan hukumonin kasar a ran 31 ga wata Mayu a kasar Korea ta Kudu, zaben da za a yi zai ba da muhimmin tasiri kan babban zaben shugaban kasar da za a yi, saboda haka, jam'iyyu da rukunoni daban daban na kasar sun yi dabara don neman samun goyon bayan masu kada kuri'a. Muhimman ayyukan da madam Han za ta yi a farko su ne shawo kan rikicin da ke tsakanin jam'iyyar da ke mulkin kasar da kuma jam'iyyun da ba su mulkin kasar, da kuma samun goyon baya daga majalisar dokokin kasar wajen harkokin cikin gida da diplomasiyya. Gogayyar diplomasiyya da aka samu tsakanin kasashen kasar Korea ta Kudu da Japan a kwanan baya kalubale ne na farko da madam Han take fuskanta bayan da ta fara aikinta. Game da wannan, a gun taron musamman da aka yi, madam Han ta bayyana cewa, za ta saurari shawarce-shawarce na masana.(Tasallah)
|