Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-25 10:42:13    
Mr Hu Jintao ya yi shawarwari da sarki na 6 na kasar Morocco

cri

A ran 24 ga wannan wata a birnin Rabat, hedkwatar kasar Morocco, shugabna kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Morocco ya yi shawarwari da S.Le Roi Mohammed Vi ,sarki na 6 na kasar Morocco.

A lokacin ganawar , Mr Hu Jintao ya nuna yabo sosai ga kasar Morocco saboda kullum take tsayawa tsayin daka a kan manufar Sin daya tak da kuma nuna goyon baya ga babban sha'anin kasar Sin na dinkuwar kasa gu daya. Don sa kaimi ga ci gaba da zurfafa bunkasuwar hadin guiwar sada zumunta a fannoni daban daban a tsakanin kasashen biyu, Mr Hu Jintao ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin yana son yin kokari sosai tare da na kasar Morocco, na farko, ci gaba da yin ma'amala a tsakanin manyan shugabannin bangarorin biyu da kuma kara habaka musayar a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu da majalisun biyu da jam'iyyun biyu, kara yin shawarwari da ba da taimakon juna wajen harkokin kasa da kasa da na shiyya shiyya da kuma sa kaimi ga yin hadin guiwar sada zumunta a tsakanin kasashen biyu. Na biyu, daukar matakai don kara habaka cinikayyar da ke tsakanin bangarorin biyu da kuma kara fannonin yin hadin guiwa da himmantar da masana'anatun bangarorin biyu wajen zuba wa juna jari. Na uku, ci gaba da sa kaimi ga yin hadin guiwa wajen ba da ilmi da al'adu da kiwon lafiya da yawon shakatawa da sauransu.(Halima)