Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-24 17:17:52    
Tsanancewar bambancin ra'ayi tsakanin kasashen Rasha da Amurka kan maganar nukiliya ta Iran

cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha Mr. Mikhail Kamynin ya bayar da wata sanarwa jiya Alhamis a Moscow cewa, lallai babu makama ko kadan a fannin dokokin shari'a bisa bukatar da kasar Amurka ta bai wa kasar Rasha ta dakatar da yin hadin gwiwa tsakaninta da kasar Iran a fannin gina tashar ba da lantarki mai aiki da karfin nukiliya taBushenr. Wassu manazarta sun ce wannan dai ya shaida, cewa ya kasance da tsanancewar bambancin ra'ayi tsakanin kasashen Rasha da Amurka kan wannan magana sakamakon rashin saurin warware maganar nukiliya ta Iran.

Kasar Amurka ta gabatar da wannan bukata ne sakamakon rashin cimma matsaya a gun teburin shawarwari kan maganar nukiliya ta Iran da aka yi tsakanin wakilan kasashen Amurka, da Rasha, da Sin, da Fransa, da Burtaniya da kuma na Jamus shekaranjiya a Moscow. Jiya Alhamis, mataimakin sakataren harkokin waje mai kula da harkokin siyasa na kasar Amurka Mr. Nicholas Burns ya nemi kasar Rasha da ta dakatar da yin hadin gwiwa tsakaninta da kasar Iran a fannin nukiliya, ciki har da aikin gina tashar ba da lantarki mai aiki da karfin nukiliya ; Dadin dadawa, ya yi fatan dukan kasashe za su dakatar da sayar wa kasar Iran hajjojin zaman yau da kullum da na soja.

Game da wannan lamari dai, Mr. Kamynin ya ce, sai dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ne kawai yake da ikon yanke shawara kan dakatar da yin hadin gwiwa tare da wata kasa a wani fanni ; amma kawo yanzu, kwamitin sulhun bai tsaida kudurin dakatar da yin hadin gwiwa tare da kasar Iran a fannin makamashin nukiliya ba tukuna. Kazalika, ya jaddada, cewa wannan tashar samar da lantarki mai aiki da karfin nukiliya ba ta da nasaba ko kadan da harkar inganta sinadarin Uranium ta kasar Iran.

A sa'i daya kuma, babban hafsan-hafsoshin rundunar soja ta kasar Rasha wato Yuri Baluyevsky ya yi shawarwari tare da janar Richard Johns na Amurka wanda kuma shi ne babban kwamandan sojojin kawanya ta Turai a ran 19 ga watan nan a Moscow, inda ya bayyana, cewa da zarar aka yi dauki ba dadi tsakanin kasashen Amurka da Iran, to Rasha ba za ta goyi bayan kowanensu ba ;

Sanin kowa ne, rashin habaka makaman nukiliya ita ce daya daga cikin muhimman ka'idoji na kasa da kasa, wadanda dukkan kasashen duniya suka amince da su. Yin Allah wadai da yunkurin bunkasa makaman nukiliya da kasar Iran ke gudanar da shi, babu tantama wannan ya zama matsayi iri daya da kasashen duniya ciki har da kasar Rasha suka dauka ; Amma kuwa, warware maganar nukiliya ta kasar Iran ta wace hanya kuma wane irin ra'ayi, wannan dai yana danganta da moriya da kuma manufofin harkokin waje na kowace kasa. Kasar Rasha da kuma sauran kasashe suna bin ka'idar shimfida demokuradiyya da zaman daidaici tsakanin kasa da kasa game da maganar nukiliya ta Iran, wato ke nan suna tsayawa kan matsayin daidaita wannan magana ta hanyar siyasa maimakon kurarin garkama takunkumi ko nuna karfin soja da kasar Amurka take son  yi.

Wassu mashahuran mazanarta sun fadi , cewa bambancin ra'ayin dake kasancewa tsakanin kasashen Rasha da Amurka a kan maganar nukiliya ta Iran ya bayyana bambancin fa'ida da kuma muhimman tsare-tsarensu. Ana gain cewa, kasar Amurka ta gama kanta da wassu muhimman manyan kasashe kan maganar nukiliya ta Iran don tilasta ta da ta yi tashin hankali da ita, ta yadda za a hana kasar Iran mallakar makaman nukiliya don kiyaye kwanciyar hankali da kuma moriya na kasar Amurka ta kanta da kuma kara tabbatar da matsayin fin karfi a duniya ; Amma a nata bangaren, da yake kasar Rasha tana da babbar moriya a fannin tattalin arziki da muhimman tsare-tsare a kasar Iran, shi ya sa ta yin adawa da yunkurin garkama takunkumi da kuma daukar matakin soja kan kasar Iran ;

Ana sa ran cewa , da kyar ne za  a kawar da bambancin ra'ayi tsakanin kasashen Rasha da Amurka kan maganar daidaita rikicin nukiliya ta Iran. ( Sani Wang )