Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-24 14:37:31    
Jakadan kasar Sin dake kasar Kenya ya yi zance kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya

cri

Daga ran 27 zuwa ran 29 ga watan nan da muke ciki,shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao zai kai ziyarar aiki a kasar Kenya.Kwanan baya, jakadan kasar Sin dake kasar Kenya ya gana da maneman labaru na rediyonmu. Yanzu za mu gabatar muku da abubuwan da wakilanmu suka rubuto mana filla filla.

Jakada ya ce, zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya yana da dogon tarihi, wato daga shekara ta l405, wani shahararren mai yin tariya kan teku Mr.Zheng he ya ba da jagora ga wani gwanon jiragen ruwa har sun kai ziyara ga tashar birnin Mombasa da Malindi na kasar Kenya.Bugu da kari kuma a ran 14 ga watan Disamba na shekara ta l963, kasar Kenya ta kulla huldar diplomasiya tare da kasar Sin. Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya, dangantakar dake tsakanin kasashe biyu tana nan tana kara samun bunkasuwa sosai. Ga wannan jakada ya fadi cewa, cikin 'yan shekaru da suka shige,manyan jami'ai na kasashe biyu sun dinga kai wa juna ziyara, har an sami babban sakamako. A watan October na shekara 2004, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya kai ziyara ga kasar Kenya. Kafin wannan, a watan Disamba na shekara ta 2003, takanas ne mataimakin shugaban majalisar ya je kasar Kenya don hallartar shagulgulan murnar ranar cikon shekaru 40 da aka kafa huldar diplomasiya a tsakanin kasashe biyu.

A ran l7 ga watan Augusta na shekarar da ta shige, a lokacin da shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao yake ganawa da shugaban kasar Kenya dake yin ziyara a kasar Sin sai ya bayyana cewa, zurfafa da kara karfi kan kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wani muhimmin kashi ne dake cikin manufar harkokin waje ta kasar Sin. Kuma kasar Sin tana son tare da kasashen Afrika ciki har da kasar Kenya za su ingiza dangantakar abokantaka ta sabon salo dake tsakaninsu zuwa wani matsayin koli.

Wannan jakada ya ci gaba da cewa, kafin shekaru 50 da suka shige, da farko ne kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya tare da kasar Massar, wannan ya kago misalin koyo kan harkokin waje dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.Kuma a watan Janairu na shekarar nan da muke ciki, da gaske ne gwamnatin kasar Sin ta bayar da wata"takardar kan manufar da gwamnatin kasar Sin take bi kan kasashen Afrika".Wannan karo na farko ne da kasar Sin ta bayar da takardar manufa ga kasashen Afrika

Jakadan ya ci gaba da cewa, a shekara ta 2005,jimlar kudin da aka samu daga cinikin da aka yi tsakanin kasashe biyu sun kai dollar Amurka miliyan 475. Tun bayan da aka kafa huldar diplomasiya tsakanin kasashe biyu har zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta ba da taimakon tattalin arziki a jere ga gwamnatin kasar Kenya, kuma cikin dukkan taimakon da kasar Sin ta ba da ba a tare da wani sharadi ba ko kadan, duk wannan ya bayyana babban zumuncin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka bayyana wa gwamnatin kasar Kenya da jama'arta.

Ban da haka kuma, kasar Sin da kasar Kenya suna nan suna kara yin musanye musanye kan al'adu da aikin ba da ilmi da na sauran sassa. Kuma a ran 28 ga watan Janairu na shekarar nan da muke ciki, rediyon kasar Sin ya kafa tashar watsa labaru ta hanyar internet a hedkwatar kasar Kenya, wannan shi ne babban sha'anin da aka yi kan tarihin yin musanye musanyen al'adu tsakanin kasashe biyu.(Dije)