Ran 22 ga wata da maraice, shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Saudiyya ya yi shawarwari tare da Abdullah Bin Abdul-Aziz, sarkin daular mulukiya ta Saudiyya a birin Riyadh. Inda suka musanya wa juna ra'ayoyinsu a kan hulda da ke tsakanin kasashensu biyu da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu duka.
Kafin shawarwarin, sarki Abdullah ya shirya gaggarumin biki don yin maraba da ziyarar da shugaba Hu Jintao ke yi.
Mr Hu Hintao ya sauka a birnin Riyadh ne bayan da ya gama ziyarar aikinsa a kasar Amurka. Ban da birnin Riyadh, Mr Hu Jintao da kungiyarsa za su zuwa birnin Dammam wato tashar jiragen ruwa mai muhimmanci a tekun Paris kuma birni mafi girma na biyu a kasaru Saudiyya don yin ziyara. (Halilu)
|