Tun daga ran 18 ga wata, shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao ya shafe kwanaki hudu yana ziyarar aikinsa a kasar Amurka. Kafofin watsa labaru na kasashen Faransa da Canada sun bayar da labarun ziyarar nan daya bayan daya, inda suka nuna babban yabo ga wannan ziyara da Mr Hu Jintao ya yi.
Jaridar mai suna "Nouvelles D'Europe" ta kasar Faransa ta buga bayanin da masharhanta ya shirya a ran 21 ga wata cewa, ziyarar Hu Jintao ta sake nuna wa jama'ar Amurka alamomin wata babbar kasa mai daukar nauyi da ke bisa wuyanta. Bayan haka bayanin ya kara da cewa, ko kusa, duk kasashe masu daukar nauyi da ke bisa wuyansu ba su yarda da a balle yankinsu daga wajensu ba. Ra'ayi da Mr Hu Jintao ya bayyana a kan batun Taiwan yayin da yake ganawa da W. Bush, shugaban kasar Amurka, sosai da sosai ya fadakar da kan Amurkawa nauyi da wannan babbar kasa ke dauke da shi bisa wuyanta.
Ban da haka kuma kafofin watsa labaru na kasar Canada su ma sun bayar da labaru filla-filla a kan wannan ziyarar da Mr Hu Jintao ya yi. (Halilu)
|