Bisa gayyatar da Abdullah Bin Abdul-Aziz, sarkin daular mulukiya ta Saudiyya ya yi masa ne, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya sauka birnin Riyadh a ran 22 ga wata da safe (Agogon Saudiyya) don fara yin ziyarar aikinsa na kwanaki biyu a kasar Saudiyya.
Bayan saukarsa a filin jirgin sama, Mr Hu Jintao ya yi jawabi a rubuce cewa, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin Sin da Saudiyya a shekarar 1990, ana ta yalwata huldar nan da ke tsakanin kasashen biyu cikin kwanciyar hankali, kuma an sami kyakkyawan sakamako wajen yin hadin guiwar tsakanin kasashen biyu a fannin siyasa da tattalin arziki da ciniki da kuma al'adu da dai sauransu. Bangaren Sin yana nuna gamsuwa ga wannan. Kasar Sin tana dora matukar muhimmanci ga yalwata hulda a tsakaninta da Saudiyya, tana son yin kokari tare da bangaren Saudiyya don kara dankon aminci a tsakaninsu da kuma kara karfin hadin guiwarsu.
A lokacin ziyararsa, Mr Hu Jintao zai yi shawarwari a tsakaninsa da Abdullah, sarkin kasar Saudiyya, kuma zai gana da sauran shugabannin kasar don musaya ra'ayoyinsu a kan hulda a tsakanin Sin da Saudiyya da matsalolin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu duka. (Halilu)
|