Ran 21 ga wata, shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao ya yi jawabi a Jami'ar Yale ta kasar Amurka, inda ya bayyana manyan tsare-tsaren raya kasar Sin ta zamani da manufar yunkurinta, bisa sauye-sauyen tarihin wayin kai na kasar Sin da bunkasuwa da take samu a yanzu.
Mr Hu Jintao ya ce, al'adar gargajiyar musamman da jama'ar Sin ta samu daga yalwatuwar dogon tarihi, ba ma kawai ta kawo tasiri ga kasar Sin ta zamanin da ba, har ma tana jawo tasiri ga kasar Sin a zamanin yanzu. Sin ta zamani ta jaddada cewa, a mayar da babbar moriyar jama'a a gaban kome, a yi ayyuka daidai da zamani, a tabbatar da zaman jituwar jama'a, kuma a sami yalwatuwa cikin lumana, duk wadannan ba ma kawai suna da tushe mai karko na wayin kai na kasar Sin ba, har ma sun nuna kyakkyawar manufa game da yalwatuwar zamani.
Bayan haka Mr Hu Jintao ya jaddada cewa, ya kasance da banbanci a tsakanin Sin da Amurka sabo da halin da suke ciki a da da yanzu ya sha banban, wannan zai taimake su da su yi koyi da juna. Kara karfin hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu ya dace da babbar moriyarsu da kuma jama'arsu, kuma yana kawo babban tasiri ga samar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.
Bayan da Mr Hu Jintao ya gama ziyarar zikinsa a kasar Amurka a ran 21 ga wata, sai ya tashi zuwa kasar Saudiyya cikin jirgin sama na musamman don ci gaba da yin ziyararsa. Daga bisani kuma, zai yi ziyara a kasar Nijeriya da Morocco da Kenya. (Halilu)
|