Ran 20 ga wata, a birnin San Francisco na kasar Amurka, madam Dianna Feinstein, kwararriyar 'yar majalisar dattijai ta kasar ta bayyana cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ke yi a kasar Amurka tana da muhimmanci sosai wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen nan 2, ya kamata kasashen Amurka da Sin su kulla dangantakar abokantaka a tsakaninsu kan wasu manyan al'amuran duniya, kana su sa kaimi kan samun moriyarsu tare.
Lokacin da take ba da lacca a gun taron shekara-shekara na kwamitin da ake kira 'the Committee of 100', wata nagartacciyar kungiyar Sinawa 'yan kaka gida ta kasar Amurka, madam Feinstein ta yi bayanin cewa, kasar Sin tana cike da imani tana kan hanyar zama kasa mai karfi da ke iya daukan nauyin da ke bisa wuyanta. Ziyarar da shugaba Hu ke yi a kasar Amurka babban batu ne a fannin bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen 2, shugabannin kasashen 2 sun yi musayar ra'ayoyinsu kan manyan batutuwa.(Tasallah)
|