Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-21 18:30:37    
Hu Jintao ya gabatar da ra'ayoyi shida dangane da ingiza muhimmiyar huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka daga dukan fannoni

cri
A ran 20 ga wata da dare a birnin Washington, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Amurka ya bayar da wani jawabin da ke da lakabin 'ingiza muhimmiyar huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka daga dukan fannoni' ga rukunoni masu zumunci da juna na Amurka, inda kuma ya bayar da ra'ayoyi shida dangane da ingiza muhimmiyar huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

A cikin jawabinsa, Mr.Hu ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana. Aikin da ya fi gaggawa ga kasar Sin shi ne mai da dukannin hankulanta a kan bunkasa tattalin arziki, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a. Sabo da haka, kasar Sin ta fi bukatar muhalli na zaman lafiya a duniya.

Masu sauraro, za ku iya shan cikakken bayani a kan ra'ayoyin nan shida daga baya a cikin shirinmu na 'mu leka kasar Sin', sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu.(Lubabatu Lei)