Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-21 17:11:58    
Masu zuba jari tare da fuskantar hadari suna da sha'awar zuba jari a masana'antun da ke samun bunkasuwa cikin sauri a kasar Sin

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, domin tattalin arzikin kasar Sin yana ta samun ci gaba a cikin hali mai dorewa, a kowace shekara, sabbin masana'antu iri iri sun bulla. Wasu masana'antu daga cikinsu wadanda suke samun riba sosai kuma suke da makoma mai haske sun jawo hankulan masu zuba jari tare da fuskantar hadari na kasar Sin da na kasashen waje.

Yankin raya masana'antun kimiyya da fasaha na Zhongguancun da ke nan birnin Beijing cibiyar kirkirar sabbin fasahohi mafi muhimmanci ce a nan kasar Sin. Yanzu akwai masana'antu dubu 17 suna yankin Zhongguancun. Galibinsu jariran kamfanoni ne da ke neman bunkasuwa.

Lokacin da yake ganawa da wakilinmu, Mr. Guo Hong, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin yankin raya masana'antun kimiyya da fasaha na Zhongguancun ya ce, a cikin shekaru 2 da suka wuce, an kafa sabbin masana'antu dubu 4 a kowace shekara. Sabbin masana'antun da suka samu kudin Renminbi yuan fiye da miliyan dari 1 wajen sayar da kayayyakinsu sun kai dari 1 a kowace shekara. Sannan kuma, jimlar masana'antun da suka samu kudin Renminbi yuan fiye da miliyan dari 1 wajen sayar da kayayyakinsu sun kai kusan dari 6 a cikin yankin. Wadannan masana'antu wadanda suke samun ci gaba cikin sauri suna jawo hankulan hukumomi masu zuba jari tare da fuskantar hadari na kasashen waje. Mr. Guo ya ce, "Kididdigar da aka yi game da jarin da aka zuba a kan sabbin jariran masana'antun ta bayyana cewa, a shekarar bara, masana'antun birnin Beijing da suka samu jarin dolar Amurka kimanin miliyan dari 3 da dubu 780 daga kasashen waje sun kai 72. Wannan adadi yana gaba a duk kasar Sin."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sana'ar shafin Internet da ta GSM da sana'ar sarrafa manhaja sun samu bunkasuwa cikin sauri a nan kasar Sin. Wasu masana'antun da ke tafiyar da wadannan sana'o'i kuma ke samun bunkasuwa cikin sauri sun jawo hankulan hukumomin zuba jari tare da fuskantar hadari na kasashen waje. Yanzu sun riga sun zama masana'anatun da hukumomin zuba jari tare da fuskantar hadari na kasashen waje suka fi son zuba jari a ciki. Domin ana samun riba sosai daga wadannan sabbin masana'antu masu samun bunkasuwa cikin sauri, bi da bi ne hukumomin zuba jari tare da fuskantar hadari na kasashen waje suka shigo kasuwar kasar Sin domin neman masana'antun da ke da boyayyen karfin samun bunkasuwa.

Mr. Li Jianguang, mataimakin babban direktan asusun zuba jari a masana'antun kirkirar sabbin fasaha a rukunin IDG na kasar Amurka ya gaya wa wakilinmu cewa, "Muhimman sana'o'in da muke zuba jari a kai su ne sana'ar IT. Da farko dai muna zubawa a kamfanin shafin Internet, sannan kuma muna zuba jari a fannonin GSM domin neman karuwar riba, wato za mu iya kara samun riba ta GSM da shafin Internet. Bugu da kari kuma, muna zuba jari a sana'ar sarrafa manhaja yayin da muke zuba jari a kan ayyukan sadarwa da ke shafar hidima da fasaha."

Ya zuwa yanzu, yawan hukumomin zuba jari tare da fuskantar hadari na kasashen waje da suke neman damar zuba jari ya riga ya kai fiye da 30. Wadannan hukumomi suna kunshe ne da rukunin WIHARPER da Soft Bank na kasar Japan da Goldman Sachs da IDG na kasar Amurka. Yawancinsu suna neman dama ne a yankunan da ke raya tattalin arziki cikin sauri da yankunan raya masana'antun kimiyya da fasaha.

Ba ma kawai masana'antun da ke samun bunkasuwa cikin sauri suna jawo hankulan hukumomin zuba jari tare da fuskantar hadari na kasashen waje kawai ba, har ma suna jawo hankulan hukumomin zuba jari tare da fuskantar hadari na cikin gida na kasar Sin. Kamfanin Infotech kamfanin kasar Sin ne da aka kafa shi a shekara ta 2000 yana zuba jari tare da fuskantar hadari. Sana'o'in da yake zuba jari suna kunshe da sana'o'in sarrafa manhaja da kayayyakin lantarki da dai makamatansu. Mr. Zhou Ning, mataimakin babban direktan kamfanin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Mun riga mun zuba jari a kan wasu ayyuka. Daya daga cikinsu ya riga ya fara sayar da takardun hannun jari a kasuwar Nasdaq ta kasar Amurka a shekarar bara. Wannan al'amari ne mai kyau. Za mu iya samun riba sosai daga wannan aiki."

Lokacin da masu zuba jari tare da fuskantar hadari na kasar Sin da na kasashen waje suke neman damar zuba jari tare da fuskantar hadari, hukumomin gwamnati da masana'antu na kasar Sin suna kuma kyautata sharuda domin neman irin wannan jarin da ake zubawa tare da fuskantar hadari. Ana fatan irin wannan jari zai bayar da taimako ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. (Sanusi Chen)