A ran 19 ga wata, an bude taron kungiyar WTO wato kungiyar ciniki ta duniya a birnin Geneva, inda karo na farko ne aka dudduba manufofin ciniki na kasar Sin. Kungiyar wakilan kasar Sin da ke karkashin shugabancin Yi Xiaozhun, mataimakin ministan kasuwanci na kasar ta hallarci taron.
Cikin jawabin da Mr. Yi ya yi ya bayyana cewa, tun shekaru 4 da suka wuce na bayan kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO, tattalin arzikin kasar ta samu bunkasuwa da sauri kuma cikin hali mai dorewa, ta gabatar da kasuwanni masu fadi ga kasashe daban- daban na duniya, kuma ta samar da babban zarafi ta hanyar zuba jari, sa'an nan kuma ta kaddamar da hajjoji masu inganci kuma masu araha ga masu sayen kayayyakin. Kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen aiwatar da alkawuran da ta dauka a lokacin da ta shiga cikin kungiyar WTO, kuma tana tsayawa kan ra'ayin cewa ya kamata a daidaita sabane-sabanen da ke tsakanin kasashe daban-daban wajen yin ciniki bisa manufofin da ka'idojin kungiyar. Hakikanan abubuwa sun ba da shaida cewa, kasar Sin wata mamba ce wadda take daukar nauyi bisa wuyanta, ta zama muhimmin karfi domin tabbatar da wadatuwa tare da sa kaimi ga shimfida zaman lafiyar duniya.
Jakadan kasar Colombia, kuma shubaban babban taron, da jakadan kasar Singapore, mai yin jagora ga babban taron, da wakilan da suka zo daga kasashe mambobin kungiyar ciki har da Indiya da Chile da Brazil da Mexico da Amurka da kawancen kasashen Turai da Canada da Australiya da Japan da Switzerland dukkansu sun girmama nasarorin da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki sosai. Sun kuma bayyana cewa, kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO ba ma kawai ta sa kaimi ga yunkurinta wajen yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ba, hatta ma ta jawo zarafi ga duniya, kasar Sin ta dauki alkawarin da ta yi, kuma ta ba da babban taimako ga tsarin yin ciniki tsakanin gefuna da yawa. Wakilan kasashe daban-daban kuma sun yi yabo ga kasar Sin sabo da babban taimakon da ta bayar a gun shawarwarin zagaye na Doha.
Kungiyar WTO da kasar Sin sun shafe shekaru 2 suna yin ayyukan share a fage domin wannan taro. Sakatariyar kungiyar ta rubuta shirin rahoto na farko na "dudduba manufofin ciniki na kasar Sin" wanda tsawonsa ya kai shafoffi fiye da 300, wanda a ciki kuma an bayyana tsari da kuma manufofin tattalin arziki da ciniki na kasar Sin filla-filla. Rahoton ya ce, bayan kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO, ta kara saurin yin gyare-gyare wajen manufofin yin ciniki da zuba jari, wannan kuwa ya kara saurin haduwar kasar Sin da duniya wajen tattalin arziki. Rahoton kuma ya sa lura cewa, kasar Sin tana son daidaita matsaloli daban-daban da take gamuwa da su wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar yin gyare-gyaren tsarin kasar.
Aikin dudduba manufofin ciniki na kasashe mambobi daban- daban cikin kayadadden lokaci ya zama daya daga cikin muhimman ayyukan da kungiyar WTO ta yi, makasudinta shi ne don sa kaimi ga fahintar juna a tsakaninsu wajen tsari da manufofin tattalin arziki da ciniki, da kara yin bayani kan manufofin ciniki na kasashe mambobi daban-daban. Ya kamata dukkan kasashe mambobin kungiyar WTO su amince da duddubawa da aka yi musu wajen manufofin ciniki cikin kayadadden lokaci bisa jerin sunayen da aka yi musu wajen ciniki.
Za a shafe kwanaki 2 ana duddubawa manufofin ciniki na kasar Sin. (Umaru)
|