
A ran 21 ga wata, hukumar binciken inganci kayayyaki ta kasar Sin ta bayar da wata sanarwa inda ta ce, daga ran 1 ga watan Mayu na bana, babban yankin kasar Sin zai kara shigar da 'ya 'yan itatuwa da kayayyakin lambu da kayayyakin ruwa daga Taiwan na kasar Sin.
Sanarwar ta ce, a lokacin yawan 'ya 'yan itatuwa da babban yanki zai shigar da su zai karu daga 18 zuwa 22, haka kuma yawan kayayyakin lambu zai kai 11, haka kuma za a yarda da shigar da kayayyakin ruwa na Taiwan zuwa lardin Fujian ba tare da bayar da takardar bayanin inganci da sassan Taiwan suka bayar ba. Ban da wannan kuma, hukumar binciken ingancin kayayyaki ta kasar Sin za ta saukaka matakan bincike da aka dauka a kan wadannan kayayyaki domin tabbatar da lafiyarsu da kara sa kaimi ga bunkasuwar cinikayya da ke tsakanin gabobi biyu.(Danladi)
|