Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-20 22:41:21    
W.Bush ya shirya gaggarumin biki don maraba da zuwan shugaban kasar Sin Hu Jintao

cri

A ran 20 ga wannan wata da safe a filin ciyawa na kudancin fadar White House na kasar Amurka , shugaban kasar Amurka W. Bush ya yi gaggarumin bikin maraba da zuwan shugaban kasar Sin Hu Jintao a kasar Amurka.

A agogon gabashin kasar Amurka da karfe 9 da rabi, shugaba Hu Jintao da shugaba W.Bush sun hau dakalin dudduba faratin ban girma, kungiyar kide-kide ta kada taken kasar Sin da na Amurka , an kuma harba bindigogi sau 21,tare da shugaba W. Bush ne shugaba Hu ya dudduba faratin girmamawa.

Shugaba Bush da shugaba Hu kowanensu ya bayar da jawabin fatan alheri.

Mataimakinn shugaban kasar Amurka Ceny da matarsa da Conzaleza race, sakatariyar harkokin waje da ministan tsaron gida Ramsfeld da sauran manya na kasar Amurka sun halarci bikin.

Mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin Tang Jiaxuan da ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing da derektan kwamitin yin kwaskwarima da raya kasa na kasar Sin Ma Kai da ministan kasuwanci Bo Xilai wadanda suke ruba wa Hu Jintao baya su ma sun halarci bikin.

Bayan bikin, shugaba Bush da shugaba Hu Jintao sun soma yin shawarwari a tsakaninsu.(Halima)