Lokacin da suke zantawa da wakilinmu na Gidan Rediyon kasar Sin a ran 20 ga wata, wasu masanan kasar Sin sun darajanta ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao yake yi a kasar Amurka.
Mataimakin shugaban kwalejin dangantakar da ke tsakanin kasashen duniya na jami'ar Jama'ar kasar Sin Mr. Jin Canrong ya bayyana cewa, ziyarar da Mr. Hu yake yi a kasar Amurka ta kara karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, ta kuma samar da sharadi ga manyan jami'ansu wajen yin cudanya a tsakaninsu a nan gaba.
Shehun malami na jami'ar ilmin tsaron kasa ta kasar Sin Mr. Pan Zhenqiang yana ganin cewa, ya kamata a yaba wa rawar da ziyarar shugaba Hu ta taka sosai. Yin cudanya tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka yana da muhimmanci wajen kara karfin huldar da ke tsakanin kasashen 2 da kuma kawar da shakkar da suke nuna wa juna a fannin muhimman tsare-tsare.(Tasallah)
|