Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-20 17:19:05    
Ganawa tsakanin Hu Jintao da manazartan kasashen Sin da Amurka

cri

Jiya Laraba, a Seattle na kasar Amurka, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da manazartan kasashen biyu wato Sin da Amurka, wadanda suke halartar taron kara wa juna sani kan hanyar da kasar Sin take bi wajen raya kasa cikin lumana da kuma makomar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, inda ya yi jawabin, cewa kasar Sin ta tsaya tsayin daka ta bi hanyar raya kasa cikin lumana. A cewarsa, kasar Sin dake yin yunkurin samun bunkasuwa cikin lumana, ta kasance tamkar muhimmin karfi na ingiza zaman lafiya, da zaman karko da kuma wadatuwa na shiyyar Asiya da tekun Pacific da na duniya; haka kuma za ta samar da kyakkyawar dama irin na tarihi ga yalwata dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Sa'annan Hu Jintao ya jaddada, cewa sai dai da gaske ne aka gane hanyar da kasar Sin take bi wajen raya kasa cikin lumana ne, za a iya fahimtar makomar kasar Sin sosai, da cin moriya iri daya ta muhimman tsare-tsare dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu da kuma daukaka ci gaban huldar dake tsakaninsu lami-lafiya.

A wannan rana, Hu Jintao ya kuma ziyarci ma'aikatar harhada manyan jiragen sama ta kamfanin Boeing, inda ya yi fatan hadin gwiwar da kasashen Sin da Amurka suke yi tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya zai kara karfi kuma da saurin gaske kamar yadda jirgin saman Boeing yake zirga-zirga;

Kafofin wasa labarai na kasashen Burtaniya da kuma Jamus sun mai da hankulansu sosai kan ziyarar da shugaba Hu Jintao yake yi yanzu a kasar Amurka. ( Sani Wang )