Ran 19 ga wata, a birnin Seattle na kasar Amurka, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya halarci dinar rana da bangarorin masana'antu da kasuwanci da kungiyoyin sada zumunta na jihar Washington da birnin Seattle suka shirya, kuma ya yi jawabi mai muhimmanci a karkashin lakabi haka "kara karfin hadin guiwa don moriyar juna da gaggauta bunkasuwa tare", inda ya bayyana manufofin kasar Sin da ra'ayoyinta filla filla dangane da yalwata huldar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen Sin da Amurka.
Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasashen Sin da Amurka a shekarar 1979, an sami ci gaba da sauri wajen bunkasa huldar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen biyu, yawan kudi da aka samu daga wajen ciniki a tsakaninsu ya wuce ninki 80. Yanzu, kasar Sin ta riga ta zama abokiyar ciniki mafi girma ta uku ga kasar Amurka, sa'an nan kuma ta zama babbar kasuwa da kasar Amurka ke samun ci gaba da sauri wajen sayar da kayayyakinta. Haka zalika kasar Amurka abokiyar ciniki mafi girma ce ta biyu ga kasar Sin, kuma ita ce kasuwa mafi girma da kasar Sin ke sayar da kayayyakinta. Mr Hu Jintao ya jaddada cewa, kara karfin hadin guiwa da sauri a tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki da ciniki ya kawo wa jama'arsu babbar moriya.
Game da batun rashin daidaituwar ciniki a tsakanin Sin da Amurka wanda ke jawo hankalin kasar Amurka, Mr Hu Jintao ya ce, "kasar Sin tana nacewa ga bin manufar fadada yawan kayayyaki da ake bukata a gida, kuma ta mayar da manufar nan don ta zama ginshikin raya tattalin arzikin da zaman jama'a. Kasar Sin za ta gudanar da tsarin kara ba da iznin sayar da kayayyakin Amurka da samar da hidimarta a kasuwannin kasar Sin. Sa'an nan kuma yana fatan bangaren Amurka zai yi kokarin daukar matakai wajen sassauta kayyade kayayyaki da take fitarwa zuwa kasar Sin, da rage manufofin kayyade kayan ciniki da sauransu, don sa kaimi ga fitar da kayayyakin Amurka zuwa kasar Sin, ta yadda za a daidaita batun rashin daidaituwa da aka samu wajen yin ciniki a tsakanin kasashen biyu da kyau kuma da sauri."
Kare ikon mallakar ilmi ita ce moriyar kasashe daban daban na duniya, kuma bukata ce da kasar Sin ke yi wajen gudanar da manufar yin kawaskwarimi da bude wa kasashen waje kofa, da kyautata guraben zuba jari, da kara karfinta na yin kirkire-kirkire cikin cin gashin kai. Mr Hu Jintao ya jaddada cewa, "kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare ikon mallakar ilmi da yaki da aikace-aikacen satar ikon mallakar ilmi. Kasar Sin za ta kara kyautata tsarin dokokinta game da kare ikon mallakar ilmi, za ta kara kokari wajen aiwatar da dokoki, ta yi yaki da aikace-aikacen take ikon mallakar ilmi a tsanake, ta yadda za ta kare masu ikon mallakar ilmi na kasashe daban daban da halaltacciyar moriyarsu a kasar Sin."
Darajar kudin Sin Renminbi wani batu ne da ke jawo hankalin bangaren Amurka kwarai. Mr Hu Jintao ya yi bayani a kan wannan inda ya ce, "kullum kasar Sin tana dauke da nauyi sosai da ke bisa wuyanta, tana kafa tsarin tsaida darajar kudinta bisa halin da take ciki dangane da bunkasuwar tattalin arzikinta da zaman jama'arta da manufar tabbatar da zaman lafiyar tattalin arziki da sha'anin kudi na shiyya-shiyya da duniya. Nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen yin kwaskwarima kan aikin kudi, da kyautata tsarin tsaida darajar kudin Sin Renminbi, da tsayar da darajar kudin Renminbi cikin adalci da daidaituwa."
Bayan haka Mr Hu Jintao ya gabatar da shawara cewa, kasashen Sin da Amurka za su yi kokari tare wajen gaggauta bunkasa tattalin arziki da samar da wadatuwa a shiyyar Asiya da ta tekun Pacific da duniya. Sa'an nan kuma su nuna goyon bayansu ga habaka hadin guiwa a tsakanin masana'antunsu, su daidaita batutuwa da suka samu wajen yin hadin guiwarsu. (Halilu)
|