Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, ran 18 ga wata a birnin Geneva na kasar Swiss, Mr. Sun Zhenyu, wakilin din din din na kasar Sin da ke kungiyar WTO ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan ayyukan duddubawa da kungiyar WTO za ta yi wa manufar ciniki ta kasar Sin; kuma kasar Sin tana cika alkawarinta cikin tsanaki lokacin da ake shigar da ita cikin kungiyar WTO. Yanzu, ga cikakken bayyani:
Bisa yarjejeniyoyin da abin ya shafa na kungiyar WTO, daga ran 19 zuwa ran 21ga wata, mambobin kungiyar za su dudduba manufar ciniki ta kasar Sin a dukan fannoni. Wannan ne karo na farko tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO a cikin shekaru 4 da wani abu da suka wuce. Gwamnatin kasar Sin ta aika da wata babbar kungiyar wakilai, wadda ke hade da hukumomin da abin ya shafa, domin wannan ayyukan duddubawa.
Kan ra'ayoyin kasashe mambobin kungiyar da na kasar Sin kan wannan ayyukan dudduba, Mr. Sun Zhenyu ya ce, "A takaice dai, kasashe mambobi suna yin jinjina sosai kan amfanin da kasar Sin ke bayar wajen ciniki da tattalin arziki na duniya, da kuma cika alkawari. Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan wannan ayyukan dudduba manufar ciniki, kuma tana fatan ta wannan ayyukan duddubawa, za ta iya kara kyautatta ayyukanta, da ingiza kara gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a cikin kasar, da kuma karfafa yin cudanya da fahintar juna a tsakaninta da kasashe mambobi."
Bayan haka kuma Mr. Sun Zhenyu ya jaddada matsaloli 3, wadanda suke iya shaida cewa, kasar Sin tana cika alkawarinta cikin hankali sosai. Kan matsalar kiyaye ikon mallakar ilmi, Mr. Sun Zhenyu ya ce, yaya za a iya kiyaye ikon mallakar ilmi wannan ne muhimmiyar matsala ta dukan kasashen duniya. Kasar Sin ta yi kokari sosai kan fannin kiyaye ikon mallakar ilmi, ta kuma kara kyautatta dokokin shari'a, da kuma kara karfin yi hukunci. Ya bayyana na musammam cewa, "Ban da yi amfani da hanyar shari'a, kuma kasar Sin ta gudanar da ayyukan kiyaye ikon mallakar ilmi ta harkokin aiki, wato shigar da karfin kasa cikin wannan ayyuka, ba za a iya gannin haka a wasu sauran kasashe ba."
Kan maganar yawan kudin musaya na RMB, Mr. Sun Zhenyu ya ce, kasar Sin ta yi ayyuka bisa alkwarin da ta yi wa asusun ba da lamuni na duniya wato IMF. Ya nuna cewa, "A hakika dai, kasar Sin ta yi gyare-gyare sosai. A da, yawan kudin musaya na RMB yana sa ido kan dollar Amurka, amma yanzu ba dollar Amurka kawai ba, ciki har da kudin EURO, da kuma sauran kudadde. Wannan ne muhimmin matakin da kasar Sin ta dauka."
Kan maganar kara bude kofa ga kasashen waje, Mr. Sun Zhenyu ya ce, kasar Sin ta yi kokari sosai kan dukan ayyukan bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin tana cika alkawarinta cikin hankali, inda suka hada da rage kudin kwastan, da bude sana'ar hidima.
Mr. Sun Zhenyu ya ce, ya kasance da bambancin matsayin cika alkawari, sakamakon bambancin matsayin bunkasuwar kasashe daban daban na duniya. Sabo da haka, ba a iya daukar wani ma'aunin da ke dacewa da dukan kasashe ba. Kuma tunin kasar Sin ta riga ta cika alkawari a sassan daban daban. (Bilkisu)
|