Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 19:54:02    
Hu Jintao ya gana da gwamnar jihar Washington

cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Amurka a halin yanzu, ya gana da gwamnar jihar Washington, Madam Christine Gregoire a ran 18 ga wata a birnin Seattle. Hu Jintao tare da 'yan rakiyarsa sun kuma kai ziyara a hedkwatar kamfanin Microsoft.

Lokacin da yake ganawa da Madam Gregoire, Hu Jintao ya nuna maraba ga bangarorin masana'antu da kasuwanci na jihar Washington da su karfafa mu'amala tare da bangaren kasar Sin, ta yadda za a dinga samun sabbin nasarori a hadin gwiwar da ke tsakanin jihar nan da kasar Sin a fannoni daban daban. A gun liyafar da aka kira daga baya don nuna maraba da zuwan shugaba Hu jintao, Mr.Hu ya jaddada cewa, kasashen Sin da Amurka suna da buri daya a wajen ingiza bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummarsu, kuma suna da moriya daya a wajen kiyaye zaman lafiyar duniya da ingiza karuwar tattalin arzikin duniya, muddin dai bangarorin biyu sun kula da huldar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, kuma sun girmama juna ko da yaushe, to, tabbas ne za a tabbatar da samun moriyar juna da nasarori tare.(Lubabatu Lei)