Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 17:16:25    
Uranium da makaman nukiliya da kuma makamashin nukiliya

cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum. Barkanmu da sake saduwa da ku a zaurenmu na amsoshin wasikunku, wato shiri ne da ke amsa tambayoyin masu sauraronmu, wanda ni Lubabatu ke gabatar muku a ko wace ranar Lahadi bayan labaru. Masu sauraro, kwanan baya, mai sauraronmu daga garin Kauran Namoda na jihar Zamfara ta kasar Nijeriya, malama Fatimah Bint Bashir ta aiko mana Email, inda ta yi mana tambayar cewa, shin mene ne karfin sinadarin Uranium a wajen kere-keren makaman nukiliya da kuma samar da makamashin nukiliya? Sabo da haka, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu ba ku dan karamin ilmi a kan Uranium da makaman nukiliya da kuma makamashin nukiliya.

Kome da kome a duniyarmu cike suke da atom iri iri, irin wannan atom ba a iya ganinsu, sai dai da madubin likita. Irin wannan atom dai, ya kan karkasu cikin gida gida, wato akwai abin da muke kira proton da kuma neutron, wadanda su biyu suka hadu suka yi nucleus na atom. Uranium dai atom ne da ya fi nauyi a duniya. A shekaru fiye da 50 da suka wuce, masanan ilmin kimiyya sun gano wani irin uranium mai nau'in U-235 wanda ke iya fashewa idan ya ci wani neutron, kuma a sa'in da yake fashewa, yana fitar da makamashi masu yawan gaske, wato aikin da muke kira nuclear fission ke nan. Idan uranium ya fashe, zai iya fitar da makamashi masu yawan gaske, alal misali, idan mun kwatanta shi da kwal, yawan makamashin da U-235 gram 1 ke iya fitarwa ya tashi daya da makamashin da kwal masu inganci da nauyinsu ya kai ton 2 da rabi ke iya fitarwa idan an kone su kwata kwata. To, irin makamashi mai yawan gaske da ake iya samu daga aikin nan na nuclear fission shi ne makamashin nukiliya. Atom bom shi ne ke amfani da irin dimbin makamashin da ake samu daga fashewar atom a wajen kawo barna, a sa'i daya kuma, na'urorin sarrafa nukiliya su ma suna amfani da wannan aiki a wajen samun makamashi, amma bambanci shi ne ana iya sarrafa su.

Makaman nukiliya sun fito ne a sakamakon bunkasuwar kimiyya da fasaha a shekarun 1940. Makaman nukiliya su ne ke amfani da makamashi masu yawan gaske da ake iya samu cikin dan lokaci daga aikin nan na nuclear fission a jere a wajen kawo barna kwarai da gaske. Yawan makamashin da makaman nukiliya ke iya bayarwa ya fi na makaman da ke da albarushi sosai. Uranium da yawansa ya kai kilogram daya yana iya ba da karfi tamkar na albarushin nan na TNT har ton dubu 20. Ba ma kawai dimbin makamashi ne makamin nukiliya ke iya bayarwa a lokacin da yake fashewa ba, har ma yana iya fitar da wuta, kuma yana iya yin tartsatsin haske iri daban daban. Wadannan halaye sun sa makaman nukiliya suka bambanta da sauran makaman da ake amfani da su a yau da kullum, har ma suna iya kawo barna sosai.

Amma ban da makaman nukiliya, uranium kuma ya kawo mana wani irin sabon makamashi mai inganci, wato makamashin nukiliya. Makamashin nukiliya makamashi ne mai tsabta. A halin yanzu dai, akasarin matsalolin da muke fuskanta a wajen gurbacewar yanayi sun zo ne daga makamashin ma'adinai. Sabo da ma'adinai suna iya fitar da hayaki da iska masu guba a lokacin da ake kona su. Iskar nan da muke kira Carbon Dioxide da dai sauran iska masu guba suna iya haddasa dumamar yanayi, wato zai sa zafin yanayin duniyarmu ya yi ta karuwa, kuma zai kara saurin kwararowar hamada, duk wadannan sun kawo masifa a kan dawamammiyar bunkasuwar zaman al'umma da tattalin arziki. Amma a nasu wajen, tashoshin nukiliya na samar da lantarki ba su fitar da irin wadannan iska masu guba, balle ma su kawo dumamar yanayi. Shi ya sa suna iya kiyaye muhallin dan Adam. A sa'i daya kuma, makamashin nukiliya makamashi ne na tattali. Bisa kidayar da kasashen da ke da tashoshin nukiliya na samar da lantarki suka yi a cikin shekaru da dama, an ce, ko da yake an fi zuba jari a wajen kafa tashoshin nukiliya na samar da lantarki, amma duk da haka, a zahiri dai, kudaden da ake kashewa a wajen samun makamashin nukiliya sun yi kasa da na kwal. Sabo da haka, gaba daya ba a kashe kudade masu yawa a wajen bunkasa lantarki da tashoshin nukiliya ba in an kwatanta shi da na tashoshin kwal na samar da lantarki.(Lubabatu Lei)