A kwanakin baya, hukumomin na gwamnaitn kasar Sin sun bayar da sanarwa don bukaci kamfannonin da ke yi computer sun ajiye software na Windows na gaskiya kafin sun sayar su. Yau bari mu yi tattaunawa a kan wannan tare da ku.
'Yan makarantun firamare da na sakandare suna iya samun ilimi iri iri ta hanyoyin sadarwa da dama,suna iya amfani da hanyoyin sadarwa na internet,suna iya kallon shirye-shiryen gidan telebiji ko kuma suna iya kallon fayefayen vidiyo.Amma a wasu yankuna masu fama da talauci na karkara na kasar Sin,hanyoyin samun labarai kadan ne ga mallaman koyarwa da 'yan makarantun firamare da sakandare da ke cikin wannan bangaren.Yau shekaru biyu ke nan da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da wani shirin samar da ilimi ta hanyar sadarwa domin canza wannan halin da wadansu yankunan kasar Sin ke ciki.
Kwanakin baya ba da dadewa ba wakilin gidan rediyonmu ya ziyarci wata gunduma dake fama da talauci da ake kira Mengying a lardin Shandong na gabashin kasar Sin.A cikin shirinmu na yau za mu dan gutsura muku wani bayanin da ya rubuto mana kan yadda ake bayar da ilimin firamare ta hanyar sadarwa a wannan gunduma..
Makarantar firamare ta Zhongxin a garin Changlu wata makarantar firamare ce da a kan gani a gundumar Mengying wadda ke da almajirai sama da dari shida.Wakilin gidan rediyonmu ya gano dakunan dake amfani da injunan zamani na bayar da labarai da kuma dakunan injuna masu kwakwalwa ban da ajujuwa da dakunan karatu a cikin wannan makaranta.Shugaban makarantar nan Mista Zhang Fengxiang ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa daga shekarar 2004 ne aka fara bayar da ilimi ta hanyar sadarwa.Ya ce "Muna bayar da ilimi ne ta hanyar shirye-shiryen da gidan telebiji ya samar da kuma hanyoyin sadarwa na internet,mun kuma ba da wasu ra'ayoyi na zamani na wuraren waje da mu ko kuma na kasashen waje,mallamanmu na koyarwa suna kara kyautatta ayyukansu.
Zhang Fengxiang ya ce domin cimma burin bayar da ilimi ta hanyar sadarwa,hukumar kula da ilimi ta gundumar Mengying ta yi matukar kokari ta hanyoyi daban daban domin tattara injuna masu kwakwalwa da akwtunan rediyo mai hoto da kuma injunan DVD da injunan daukar labarai daga tauraron dan Adam da sauran kayayyakin koyarwa da ake bukata.Ga shi a yau a cikin makarantun firamare da sakandare sama da 240,yawancinsu ana iya samar da ilimi ta hanyoyin sadarwa.
Da wakilin gidan rediyonmu ya shiga dakin injuna masu kwakwalwa,sai ya ga 'yan makaranta da dama suna amfani da injuna.Wata 'yar makaranta mai shekaru goma da haihuwa da ake kira Li Xue ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa tana kishin ilimi na inji mai kwakwalwa,Yanzu tana iya amfani da injin yadda ta ga dama.ta yi magana da alfaharin cewa "na iya amfani da inji mai kwakwalwa wajen rubuta kalmomi a sassa daban daban,na iya amfani da WORD,kuma na iya zana hotuna da injin,haka kuma na iya takardun gaisuwa da injin."
Wakilin gidan rediyonmu ya kidaya yawan injunan da ke akwai a cikin aji,yawansu ya kai hamsin.Yayin da ake bayar da ilimi inji mai kwakwalwa kusan kowane dan aji yana iya samun injin daya.Sa'ad da mallamin koyarwa ya ke bayar da ilimi,'yan ajin suna iya amfani da inji kamar yadda mallaminsu ya gaya musu.Mallamin koyarwa Zhou Junxiang ya gaya wa wakilinmu cewa an fara bayar da ilimin inji mai kwakwalwa a aji na uku a wannan makaranta,an samar da darussa talatin a kalla a zangon makaranta daya.Yawancin 'yan makaranta ba su da injunan a gidajensu,shi ya sa suke son su yi amfani da injunan da ke cikin makaranta sosai.Ya ce bayan shekara daya ko fiye da haka,sai suka samu ilimi da dama a wannan fanni.
|