Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 16:31:46    
wasu labaru game da wasannin motsa jiki (13/04-19/04)

cri
Ran 16 ga watan nan, kwamitin kula da harkokin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya shelanta, cewa an rigaya an tabbatar da sunayen wadanda suke cikin kungiyar ba da jagoranci ga aikin gudanar da bikin budewa da kuma rufe taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a shekarar 2008 a nan Beijing. Sannannen mai ba da jagoranci ga nuna wasannin fasaha mai suna Zhang Yimou zai zama babban mai ba da jagoranci ga aikin gudanar da bikin budewa da kuma rufe taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ; Ban da wannan kuma, an tabbatar da kungiyar mashawarta ta fasaha, wadda take kunshe da wassu mashahuran mutane daga da'i'rar al'adu ciki har da Mr. Steven Spielberg, shahararren mai ba da jagoranci kuma mai kera filin din sinema na Hollywood.

Kwararrun mutane da yawansu ya kai 3,307 daga sana'o'i iri daban-daban na gida da na waje sun shiga jarrabawar daukar aiki bisa kwangila, wadda kwamitin kula da harkokiin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya shirya shekaranjiya ranar Lahadi a nan Beijing.

An kawo karshen gasar tseren keken hawa ta kasa da kasa a shekarar 2006 a ran 16 ga watan nan, wadda aka shafe kwanaki hudu ana yinta a

birnin Bordeaux na kasar Fransa. ' Yar wasa mai suna Guo Shuang ta samu lambobin tagulla guda biyu; Kasar Holland ta zo na daya a wajen samun lambobin zinariya.

An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan kundunbala da lankwashe-lankwashe wato gymnastic ta Pan-Tekun Pasific a ran 15 ga watan nan a Hawaii na kasar Amurka. Kungiyar wakilan kasar Sin ta samu lambobin zinariya guda hudu, da lambobin azurfa guda uku da kuma lambar tagulla guda daya. Akan yi wannan gasa ne sau daya a shekaru biyu-biyu.

A cikin gasar kusa da karshe ta cin kofin Asiya ta 3 ta wasan kwallon kafa na mata wadanda shekarunsu ba su kai 19 da haihuwa ba da aka yi a ran 15 ga watan nan a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia, kungiyar kasar Sin ta lashe ta kasar Japan da ci 5 da 3, wato ke nan ta samu damar shiga gasar karshe da za a yi da kuma iznin shiga gasar cin kofin duniya ta 3 ta wasan kwallon kafa ta samari mata da za a yi a karshen wannan shekara a kasar Rasha.

An yi nasarar yin fida kan kafar mashahurin dan wasan kwallon kwando mai suna Yao Ming na kasar Sin a ran 14 ga watan nan, wanda yake yin wasa a kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets dake yin takara a gasar NBA.( Sani Wang )