Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 16:02:45    
Kasar Sin za ta cika alkawarin kiyaye ikon mallakar ilmi a tsanake, in ji shugaba Hu Jintao

cri

Ran 18 ga wata da yamma, bisa agogon wurin, a birnin Seattle na kasar Amurka, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya ziyarci babban zauren kamfanin Microsoft. Ya kuma bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya riga ya kara karfin kiyaye ikon mallakar ilmi daga fannonin kafa dokoki da aiwatar da su, nan gaba zai cika alkawarinsa a tsanake.

Bayan ziyararsa, Mr. Hu ya yi bayanin cewa, kiyaye ikon mallakar ilmi ba ma kawai ya biya bukatar kasar Sin a fannonin kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma kyautata halin zuba jari ba, har ma, ya biya bukatar kasar Sin wajen kara karfin kirkire-kirkire da kansa da kuma samun saurin bunkasuwa lami lafiya, bangaren kasar Sin zai cika alkawarinsa a tsanake. Ya kara da cewa, kamfanin Microsoft ya yi hadin gwiwa da kasar Sin lami lafiya, ya kamata su kara yin hadin kansu, musamman ma a fannin horar da kwararru. Kasar Sin tana maraba da kamfanin Microsoft da ta kara zuba jari a kasar Sin.(Tasallah)