Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 14:42:28    
Ya zuwa yanzu, hulda a tsakanin Sudan da Chadi tana da tsanani

cri
Ran 17 ga wata, Antonio Guterres, babban kwamishinan majalisar dinkin duniya mai kula da batun 'yan gudun hijira ya tabbatar da cewa, Idriss Deby, shugaban kasar Chadi ya riga ya janye barazanar da ya yi a kan bayar da umurnin korar 'yan gudun hijira na kasar Sudan daga yankin kasarsa. Amma ya zuwa yanzu dai, kasar Chadi tana nacewa ga yanke huldar diplomasiya a tsakaninta da kasar Sudan, da kuma rufe bakin iyakar kasa da ke tsakaninsu.

Shugaba Deby ya yanke wannan shawara ne a ran 14 ga wata, bayan da sojojin gwamnatin Chadi suka murkushe farmaki da dakaru masu adawa da gwamnati suka tayar a kan birnin N'Djamena, hedkwatar kasar. Gwamnatin kasar Chadi ta bayyana cewa, wasu mambobi na kungiyar adawa da gwamnatin wadanda suka kai farmaki kan N'djamena sun fito ne daga yankin kasar Sudan. Deby ya zargi gwamnatin Sudan da daurin gindi da ta yi wa dakaru masu adawa da gwamnatin Chadi wajen tauye zaman lafiyar mulkin Chadi. Ya kuma yi barazanar cewa, idan majalisar dinkin duniya da kawancen kasashen Afrika ba su dauki matakai cikin lokaci ba wajen sarrafa zaman lafiyar bakin iyakar kasa a tsakanin Sudan da Chadi ba, to, zai bayar da umurnin korar 'yan gudun hijira da yawansu ya kai kamanin dubu 200 daga yankin kasar Chadi.

A kan zargin da bangaren Chadi ya yi, Omar Al-Bashir, shugaban kasar Sudan ya bayyana cewa, kullum kasarsa tana aiwatar da manufar rashin yin shisshigi cikin harkokin gida na sauran kasashe. Ya ce, kasarsa tana ta gudanar da yarjejeniyar da bangarorin nan biyu suka daddale a watan Febrairu da ya wuce dangane da kare zaman lafiya da zaman karko a bakin iyakar kasa da ke tsakaninsu cikin hadin guiwa, amma ko da yaushe, kasar Chadi ba ta aika da wakilanta don shiga aikin kwamitin zaman alfiya na bakin iyakar kasashen biyu ba, ta haka ba a aiwatar da yarjejeniyar nan sosai ba.

A cikin wani tsawon lokaci da ya wuce, dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Chadi suna ta fadi-tashi a wurare da ke kan bakin iyakar da ke tsakanin Chadi da Sudan, sa'an nan kuma yankin Darfur na kasar Sudan wanda ke jawo hankulan gamayyar kasa da kasa yana gabashin bakin iyakar tsakanin kasashen biyu. Kasashen Sudan da Chadi suna zargin juna da goyon baya da abokiyar gaba ke nuna wa dakaru masu adawa da gwamnati, har illa yau hulda a tsakanin kasashen biyu ta taba kai intaha a cikin wani lokaci. A ran 23 ga watan Disamba na shekarar bara, gwamnatin kasar Chadi ta bayar da sanarwa cewa, yaki ya barke a tsakanin kasashen Chadi da Sudan. Bayan haka domin shiga tsakani da kawancen kasashen Afrika ya yi, gwamnatocin kasashen nan biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Febrairu da ya wuce, sun dauki alkawarin rashin tsoma hannu cikin harkokin gidansu, ba su nuna goyon baya ga kungiyoyin 'yan tawayensu ba. Amma duk da haka ba a kawar da rashin amincewa a tsakaninsu ba.

Manazarta suna ganin cewa, ya zuwa yanzu dai, mai yiwuwa ne za a sassauta hulda mai zafi da ke tsakanin kasashen Chadi da Sudan.

Na daya, bangaren Sudan ya yi ta mayar da martani a tsanake. Ya zuwa yanzu dai, kasar Sudan ba ta nuna tsattsauran ra'ayi ga kudurin da kasar Chadi ta tsaida kan yanke hulda a tsakanin kasashen biyu ba tukuna. Banban da haka ta sha tisa magana cewa, za ta ci gaba da nuna biyayya ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka daddale a tsakanin kasashen biyu.

Na biyu, gamayyar kasa da kasa ma tana fatan za a shawo kan hali mai zafi da ake ciki dangane da hulda a tsakanin kasashen biyu tun da wuri.

Na karshe kuma, Faransa da Amurka da sauran kasashe wadanda ke taka muhimmiyar rawa a shiyyar nan su ma sun nuna ra'ayinsu kan kare zaman lafiya da zaman karko a shiyyar, ba su son ganin barkewar yaki a tsakanin kasashen Sudan da Chadi. A ran 16 ga wata, Idriss Deby, shugaban kasar Chadi ya janye barazanar da ya yi a kan bayar da umurnin korar 'yan gudun hijira na kasar Sudan daga yankin kasarsa, wannan sakamako ne ga babban kokari da gamayyar kasa da kasa ta yi. (Halilu)