Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 11:02:59    
Sinnawan dake kasashen waje sun nuna yabo sosai ga taron fadin albarkacin bakinka kan tattalin arziki da ciniki na gabobi biyu na Tekun Taiwan

cri
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , kwanan nan Sinnawan dake kasashen waje sun nuna yabo sosai ga taron fadin albarkacin bakinka da aka yi kan tattalin arziki da ciniki na gabobi biyu na Tekun Taiwan a nan birnin Beijing . Zhou Pingyao , Sakataren Kungiyar ingiza dinkuwar kasar Sin ta Ingila ya ce , a gun taron bangaren babban yanki ya gabatar da matakan manufofi guda 15don sa kaimi kan hadi kan gabobi biyu da ba da gatanci ga 'yan uwan Taiwan ya dace da moriyar jama'ar Taiwan , kuma ya bayyana cewa , muddin gabobin biyu su yalwata huldar zumunci sai jama'a su sami zaman rayuwa mai dadi .

Lian Weihong , shugaban Kungiyar ingiza dinkuwar Kasar Sin ta Canada ya bayyana cewa , Hu Jintao , shugaban kasar Sin ya gana da Lian Zhan , shugaba mai daukaka na Jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin kuma ya gabatar da shawarori 4 ga yalwatuwar hulda tsakanin gabobin biyu . Ko shakka babu za su kawo tasiri mai zurfi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da musanye-musanye tsakanin gabobi biyu . (Ado)