A ran l5 ga watan nan da muke ciki, a nan birnin Beijing, an rufe dakalin kara wa juna sani na tattalin arziki da ciniki tsakanin bangarori biyu wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa. A gun dakalin kara wa juna sani, sassa biyu sun gabatar da shawarwari tare kan kara karfi da zurfafa musanye musanye da aikatayyar tattalin arziki na tsakanin bangarori biyu.
Kuma babban yankin Sin ya gabatar da matakan manufa nuna gatanci ga 'yan uwa na yankin Taiwan a kan sassa guda l5. A ran l6 ga watan nan da muke ciki, Mr.Hu Jintao babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gana da Mr. Lien Chan shugaba mai daukaka na jam'iyyar Koumintang wato KMT. Hakikanin abubuwa suna bayyana cewa, kai wa juna moriya da yin hadin guiwa a tsakanin bangarori biyu su ne burin tare na jama'ar bangarori biyu.
A watan Afrilu na shekara ta 2005,Mr.Hu Jintao babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da Mr.Lien Chan shugaban jam'iyyar KMT sun gana da juna a karo na farko tun bayan shekaru 60 da suka shige tsakanin manyan shugabanni na jam'iyyu biyu. A gun wannan dakalin kara wa juna sani, an sami babban sakamako. A lokacin da shugaba mai daukaka na jam'iyyar KMT yake ganawa da shugaba Hu Jintao sai Mr.Lien Chan ya nuna yabo ga wannan sakamakon da aka samu cikin shawarwari sai ya bayyana cewa, ya ce, a gun wannan dakalin kara wa juna sani na karo na farko na game da tattalin arziki da ciniki, an bayyana matakan manufar nuna gatanci ga 'yan uwa na yankin Taiwan,wannan yana da babbar ma'ana.
Wata wakiliya ta jam'iyyar KMT dake halartar wannan dakalin kara wa juna sani mai suna Zhu fenzhi ta gaya wa maneman labaru cewa, ina gani cewa wadannan matakan manufar nuna gatanci ga 'yan uwa na yankin Taiwan sun nuna ban kula sosai ga 'yan uwa na yankin Taiwan.
A gun wannan dakalin kara wa juna sani kan tattalin arziki da ciniki, an sa muhimmanci sosai ga tattauna matsayin yin musanye musanyen tattalin arziki da ciniki da yin zirga zirga na jiragen sama tsakanin bangarori biyu kai tsaye.A cikin 'yan shekaru da suka shige, tattalin arziki na yankin Taiwan bai sami bunkasuwa da kyau ba, sai 'yan uwa na Taiwan suna son yin hadin guiwa tare da 'yan uwa na babban yankin kasar Sin don neman samu moriyar juna tare.
Bayan da aka gama wannan dakalin kara wa juna sani na tattalin arziki na tsakanin bangarori biyu, a nan birnin Beijing, Mr.Hu Jintao babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ya gana da Mr.Lien Chan shugaba mai daukaka na jam'iyyar KMT dake ba da jaroranci ga kungiyar wakilai na yankin Taiwan dake halartar wannan dakalin kara wa juna sani.inda Hu Jintao ya nanata cewa, koda yake ana yin sauyawar halin siyasa a yankin Taiwan, amma har abada babban yanki zai iya cika alkawarin da ya yi ga 'yan uwa na yankin Taiwan. Mr.Hu Jintao ya kuma gabatar da shawarwari guda hudu na kara bunkasa dangantakar dake tsakanin bangarori biyu.Ya ce, na farko, za mu ci gaba da tsaya kan ra'ayin daya da sassa biyu suka samu a shakara ta 92. domin wannan shi ne muhimman tushe na neman zaman lafiya da bunkasuwa na tsakanin bangarori biyu. Na biyu, sassa biyu za su yi kokarin cika babban burin jama'a na bangarori biyu. Na uku, za a kara karfi da zurfafa musanye musanye da yin aikatayya a tsakaninsu. Na hudu, za a yi shawarwari bisa matsayin daidai wa daida.(Dije)
|