Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-18 15:56:25    
Shugaban kasar Chadi ya toge barazanar zai kori 'yan gudun hijira na kasar Sudan da ya yi

cri

Ran 17 ga wata, Mr. Antonio Guterres jami'i mai kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD ya ce, shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya riga ya toge barazanar zai kori 'yan gudan hijira na kasar Sudan da ya yi a kwanakin baya.

Guterres ya ce, a ran 16 ga wata da dare ya yi tattaunawa tare da shugaba Idriss Deby ta waya, a cikin tattanawar shugaba Idriss Deby ya sake jaddada cewa kasar Chadi za ta bi dokar kasashen duniya, ba za ta kori 'yan gudun hijira da karfi.

A ran 10 ga wata, dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Chadi sun kai farmaki ga babban birni N'Djamena na kasar, kuma mutane daruruka sun mutu ko ji rauni. Ran 14 ga wata, Deby ya zargi kasar Sudan ta goyon baya dakarun, kuma kasar Chadi ta yanke huldar diplomasiyar da ke tsakanin kasashen biyu. Ya ce, idan MDD da kungiyar AU ba su dauki matakai don daidaita halin da ake cikin zirin Darfur na kasar Sudan zai ba da iznin kori 'yan gudun hijira dubu 200 na kasar Sudan da ke gidan kasar Chadi.