A ran 16 ga wata da dare, jam'iyyar Kuomintang ta bayar da sanarwar shugabanta Ma Ying-jeou cewa, nasarorin da aka samu a gun taron dandalin fadin albarkacin bakinka kan tattalin arziki da ciniki da aka yi a tsakanin babban yanki da yankin Taiwan na kasar Sin na jama'a da yawansu ya kai miliyan 23 ta Taiwan, yana fata jam'iyyar DPP za ta sa kaimi a kan haka.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na Taiwan suka bayar, an ce, jam'iyyar Kuomintang ta bayyana cewa, tabbas ne matakai 15 da babban yankin kasar Sin ya sanar da su domin samar wa Taiwan alheri a gun taron za su bayar da sababbin damar bunkasuwar tattalin arzikin Taiwan, haka kuma za su kara guraban ayyuka da jama'a suke yi. Ban da wannan kuma, manufar ziyarar da mazaunan babban yanki suka kai a Taiwan za ta kara bayar da damar yin ciniki ga sha'anin hidimma na Taiwan. A takaice dai, nasarorin da aka samu a gun taron za su zama wani tushe da gabobi biyu suka kara gama kansu a kan tattalin arziki da cinikayya, ta haka Taiwan zai iya more nasarorin da babban yankin kasar Sin ya samu wajen bunkasuwar tattalin arziki.(Danladi)
|