Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-17 17:13:57    
Kasar Cambodia mai dogon tarihi da al'adu

cri

Kasar Cambodia tana kudancin tsibirin Zhongnan, kasashen Vietnam, Laos da Thailand su ne makwabicinta, fadin kasar ya kai mura'bayin kilomita dubu 180. yawan mutanen kasar ya kai miliyan 13.4, kasar tana da kabilu fiye da 20.

Manyan duwatsun da ke wani gefen tafkin siffarsu ta yi kama da wata mace mai juna biyu da ke kwance a can. An ba wa tsibirin da tafkin suna bisa tatsuniyar haduwar wata budurwa da ba ta mutu ba da wani yarima, bayan da wannan mace ta haifi yaro na farko, ba da jimawa ba sai yaron ya mutu, ta yi bakin ciki kwarai, kuma ta bizne yaron cikin ruwan tafki mai tsabta. Kafin ta koma aljanna, ta ba da matukar karfi ga ruwan tafkin, ta yadda matan da ba sun iya haifuwa ba da su yi wanka cikin ruwan tafkin, za su iya samun haifuwa.

Tsibirin mace mai juna biyu babban tsibiri na 2 ne daga cikin tsibirorin Langkawi, a kan wannan tsibiri akwai wani tafkin ruwa mai dadi na marmaro mai kayatarwa. Kuma da akwai tatsuniyoyi masu dadin ji da yawa game da wannan tsibiri. Tatsuniya ta farko ita ce, an yi wani namiji da matarsa, bayan shekaru 19 da suka yi aure, ba su samu haifuwa ba. Wata rana matarsa ta sha ruwan tafkin, ba da dadewa ba sai ta samu juna biyu kuma ta haifi wata yarinya. Tatsuniya ta biyu ta shafi wata gimbiya wadda ta kashe kanta cikin ruwan tafkin sabo da ba ta samu wani mijin da take kauna ba. Tatsuniya ta 3 kuwa ita ce, wani namiji mai suna Mat Teja ya nuna soyayya ga wata budurwa mai suna Manbang Sari. Domin mallakar zuciyar budurwar, kowace rana lokacin da ruwan tafkin ya haura sama, sai wannan namiji ya je gabar teku don tattara hawayen mamiyota, kuma ya wanke fuskarsa da ruwan tafkin. Daga baya kuma, sun yi aure kuma sun haifi wani jariri. Amma ba su yi sa'a ba, wato bayan kwanaki 10 da aka haifi jaririn, sai ya mutu, kuma uwarsa ta jefa gawarsa cikin ruwan tafkin. Duk wadannan labaru tatsuniyoyi ne, mutane masu yawon shakatawa sun iya amincewa da haka ko a'a. Amma idan an duba tsibirin daga wani fanni sai a gane cewa, siffar tsibirin ta yi kama da wata mace mai juna biyu da ke kwance a can, wannan ya kara mai da tatsuniyoyin da su jawo hankulan mutane. Sabo da haka, tsibirin mace mai juna 2 ya samu maraba sosai daga wajen tarin matan da ba su iya samun haihuwa ba, suna fatan za su iya dandana ruwan tafkin domin samun haihuwa.

Mutane masu sha'awar yawon shakatawa a bakin teku da hawan dutse su ma sun dace da zuwa tsibirin mace mai juna biyu. Masu yawon shakatawa sun iya kashe duk rana wato daga safe zuwa yamma suna yin yawo a gabar teku da gabar tafkin, kuma sun iya dafa abinci a kan duwatsu, da kama kumba, da yin fatsa da kama tsuntsaye da malam bude littafi masu daraja, kuma sun iya more zaman jin dadi a bakin teku da ba a kwaramniya.

Tsibirorin da ke cikin tafkin mace mai juna biyu suna da ni'ima kuma ba su kwaramniya, ruwan tafkin mai launin shudi ya sa mutane farin ciki da annashuwa. A wani wurin da ke kusa da tafkin da akwai kogon dutse mai suna Gualan-sir da na Caveof Banshee, tsayin kogon ya kai mita 90, kuma da akwai jemage dubu-dubai cikin kogon mai duhu. Tsibirin nan yana jawo hankulan mutane, kuma wuri ne da masu yawon shakatawa suke son zuwa don yin bincike, hanyoyin tsibirin suna da kyau, yanayin tsibirin yana da ni'ima, idan ka yi hayar mota, za ka iya kai ziyara a duk tsibirin, a can kuma akwai lanbunan itatuwan roba da gonakin shinkafa, da shanu. Ban da wannan kuma za ka iya yin hayar babur da keken hawa yadda ka ga dama domin kallon wurare masu kyaun gani. Bayan da ka yi yawo kuma ka ji labaru masu ban mamaki, kuma ka gaji da tafiya, sai ka iya tsayawa ka huta, kuma ka kwanta a wurin rairayi da ke bakin teku domin more annashuwa.(Musa)